An samu bullar cutar Coronavirus karon farko a jahar Adamawa

An samu bullar cutar Coronavirus karon farko a jahar Adamawa

Duk da matakan kandagarki da gwamnatocin jahohi suke dauka game da yaduwar annobar Coronavirus, amma cutar na cigaba da kutsa kai lungu da sakon kasar nan.

A wannan karo, annobar ta shiga cikin jahar Adamawa, wanda hakan ya zamto karo na farko da aka samu wani mutumi mai dauke da ita tun bayan watanni biyu da fara yaduwar ta.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus: Majalisar Musulunci ta Najeriya ta bayyana abin da ya kamata a yi da gawar Musulmi

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito mutumin da ya fara kamuwa da cutar a Adamawa ya koma gida ne daga jahar Kano, inda isar sa keda wuya ya mika kansa domin a yi masa gwajin cutar.

A makon da ta gabata ne ya shiga Adamawa, kuma tun lokacin ya killace kansa yayin da yake jiran sakamakon gwajin. Sai a ranar Laraba sakamakon ya fito, kuma ta nuna ya kamu da cutar.

“Ina zaune sai kwamitin yaki da yaduwar COVID-19 ta jahar Adamawa ta kira ni a waya, ta bayyana min cewa sakamakon gwajin da aka gudanar a kai na ya nuna ina dauke da cutar.” Inji mutumin.

An samu bullar cutar Coronavirus karon farko a jahar Adamawa

An samu bullar cutar Coronavirus karon farko a jahar Adamawa
Source: Twitter

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto gwamnatin jahar bata sanar da lamarin a hukumance ba, amma majiyar ta nemi jin ta bakin sakataren gwamnatin jahar, Bashiru Ahmad.

Da jin bukatar majiyar ta mu, sai Bashiru Ahmad ya ce: “Zan sake kiran ku.” Iya maganan kenan.

A baya Legit.ng ta kawo muku wani rahoto a kan jahohin Najeriya 12 da basu samu bullar cutar Coronavirus a cikinsu ba, wanda daga cikinsu har da jahar Adamawa.

Sai dai biyo bayan bullarta a Adamawa, jahohin da suka rage sun koma 11: Bayelsa, Cross River, Ebonyi, Imo, Kebbi, Kogi, Nasarawa, Plateau, Taraba, Yobe da kuma jahar Zamfara

A yanzu haka gwamnonin Plateau, Nassarawa, Yobe da Imo sun garkame iyakokin jahohinsu babu shiga babu fita, wannan wani mataki ne na kare baki daga shigar musu da cutar.

Hukumar yaki da yaduwar cututtuka a Najeriya ta ce Coronavirus ta shiga jahohi 25 da kuma babban birnin tarayya Abuja, inda ta kama mutane 782, ta kashe 25.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel