Dakaraun Sojojin Najeriya sun yi artabu da yan bindiga, sun halaka 21 a Zamfara

Dakaraun Sojojin Najeriya sun yi artabu da yan bindiga, sun halaka 21 a Zamfara

Shelkwatar tsaro ta rundunar Sojin Najeriya ta sanar da mutuwar wasu gungun yan bindiga dadi a jahar Zamfara har guda 21 bayan wata kazamar karanbatta da suka yi da Sojoji.

Jaridar Guardian ta ruwaito shugaban sashin watsa labaru na shelkwatar, Manjo Janar John Enenche ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 21 ga watan Afrilu.

KU KARANTA: Miyagun yan bindiga sun kashe Yansanda 2 a cikin kamfanin Atiku Abubakar

John yace an yi arangamar ne a ranar 20 ga watan Afrilu a garin Zurmi, cikin karamar hukumar Zurmi na jahar Zamfara, inda dakarun Operation Hadarin Daji suka samu nasara.

“A yayin artabun, Sojojin mu sun kashe yan bindiga daidai har guda 21, yayin da zaratan Sojoji guda hudu suka mutu.” Inji shi.

Sai dai yace karin bayani game da harin zai biyo baya.

Amma John yace Sojoji sun kara kaimi wajen sintiri a yankin don mamaye yankin tare da nuna karfin iko da kuma kwantar da hankulan mazauna yankunan.

Dakaraun Sojojin Najeriya sun yi artabu da yan bindiga, sun halaka 21 a Zamfara
Dakaraun Sojojin Najeriya sun yi artabu da yan bindiga, sun halaka 21 a Zamfara
Asali: UGC

Daga karshe John ya nemi jama’a su cigaba da baiwa Sojoji hadin kai ta hanyar basu sahihan bayanan sirri da zai taimaka musu wajen kawar da miyagu daga kasar gaba daya.

A wani labari kuma, Wasu gungun yan bindiga sun kaddamar da farmaki a wani kamfanin tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar a jahar Adamawa.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito a yayin harin, yan bindigan sun kashe wasu jami’an Yansanda guda biyu da suka hada da DSP Gbenga da ASP Yohanna.

Yansandan sun kai ziyara zuwa kamfanin Atikun mai suna RicoGado ne domin duba yanayin kamfanin don sanin irin jami’an Yansandan da zasu tura domin samar da tsaro a kamfanin.

Sai dai wani dansanda da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa daga dukkan alamu an shirya kashe Yansandan ne don haka aka shirya musu tarko suka kuma fada.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel