Shugaba Buhari na bukatar a kafa kotun laifuka na musamman

Shugaba Buhari na bukatar a kafa kotun laifuka na musamman

- Shugaban Muhammadu Buhari a jiya ya shawarci Alkalin alkalan Najeriya, Jastis Ibrahim Tanko Muhammad a kan a shirya kafa kotun laifuka na musamman a dukkan jihohin Najeriya

- Buhari ya yi kira a kan gaggauta kammala shari'a tare da rage yawan mazauna gidajen gyaran hali don gujewa yaduwar annobar coronavirus

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya ya shawarci Alkalin alkalan Najeriya, Jastis Ibrahim Tanko Muhammad a kan a shirya kafa kotun laifuka na musamman a dukkan jihohin Najeriya.

Kotun laifuka na musamman din za su dinga shari'a ne da suka shafi fashi da makami, garkuwa da mutane, dabanci da sauran manyan laifukan da ke bukatar shari'ar gaggawa.

A wasikar da Buhari ya tura wa Jastis Tanko, ya ce: "Akwai bukatar alkalan jihohi da na tarayya da su bai wa kananan kotu umarnin kiyaye dokar ajiye masu laifuka ballantana wadanda kotunsu ba za ta iya yankewa hukunci ba."

Kamar yadda yace, "Wannan na nufin cewa a daina ajiye masu laifin da ke jiran hukunci a gidajen gyaran hali."

Buhari ya yi kira a kan daukar matakin gaggawa don kare shari'a tare da rage yawan mazauna gidajen gyaran hali don gujewa yaduwar annobar coronavirus a kasar nan.

Shugaba Buhari na bukatar a kafa kotun laifuka na musamman
Shugaba Buhari na bukatar a kafa kotun laifuka na musamman
Asali: UGC

KU KARANTA: Kano: 'Yan sanda sun damke limamai 15 a fadin jihar

A wani labari na daban, limamai 15 ne rundunar 'yan sandan jihar Kano ta damke a kan zarginsu da ake da yin sallar Juma'a ta jam'i a jihar tare da karya dokar hana zirga-zirga.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bada dokar hana zirga-zirga a jihar na tsawon kwanaki bakwai.

A cikin dokar kuwa, akwai haramcin taro kowanne iri har da na addinai da suka hada da sallar Juma'a da taron coci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel