An samu wani Likita da ya kamu da cutar COVID-19 a Ekiti - Kwamishinar lafiya

An samu wani Likita da ya kamu da cutar COVID-19 a Ekiti - Kwamishinar lafiya

A daidai lokacin da alkaluma su ka nuna cewa masu cutar COVID-19 sun haura mutum miliyan 2.5 a kasashen Duniya, adadin masu wannan muguwar cuta a Najeriya ya zarce 680.

Gwamnatin jihar Ekiti ta tabbatar da cewa an sake samun mai dauke da wannan cuta. Wannan karo wani Likita ne ya kamu da cutar yayin da ya ke kokarin ceto ran wata Baiwar Allah.

Kamfanin dillacin labarai na kasa watau NAN, ta ce wannan likita ya kamu da cutar COVID-19 ne yayin da ya ke lura da wata ‘yar shekara 29 mai dauke da juna biyu da ke da Coronavirus.

Wannan mata ita ce mutum ta uku da ta kamu da COVID-19 a Ekiti.

A sakamakon gogawa Likitan na ta cutar da ta yi, wadanda wannan cuta ta kama a jihar sun kai mutum hudu a yanzu.

Kwamishinar lafiyar jihar Ekiti, Dr. Mojisola Yaya-Kolade ta shaidawa ‘yan jarida wannan a lokacin da ta zanta da su a jiya ranar Talata, 21 ga watan Afrilu, 2020 a garin Ado-Ekiti.

KU KARANTA: Shugaban kungiyar Likitoci ya kamu da COVID-19 a jihar Sokoto

An samu wani Likita da ya kamu da cutar COVID-19 a Ekiti - Kwamishinae lafiya
An samu Likitan da ya kamu da cutar COVID-19 a Ekiti
Asali: Twitter

Dr. Mojisola Yaya-Kolade ta ce mutane 15 da ake zargin sun kamu da wannan cuta da aka yi gwaji. Sakamakon da ya fito jiya ya tabbatar da cewa Likitan nan ne kawai ya ta ki rashin sa'a.

“Mun samu Likita guda wanda gwaji ya nuna ya na dauke da kwayar cutar COVID-19, kuma yanzu ana lura da shi a dakin da ake killace wadanda su ka kamu da wannan cuta.” Inji ta.

Kwamishinar lafiyar ta tabbatar mana da cewa duk ragowar sauran mutanen 15 da aka yi wa gwaji ba su dauke da wannan cuta. Kawo yanzu COVOD-19 ta kashe mutane 25 a Najeriya.

Kungiyar likitocin Najeriya na reshen Ekiti ta girgiza, kuma ta yi mamaki sosai da jin wannan labari. NMA ta yi kira ga hukuma ta kare malaman jinya da ke sadaukar da rayuwarsu.

Shugaban NMA na jihar, Dr Tunji Omotayo, ya yi farin cikin samun labarin cewa sauran likitocin da ke aiki da babban asibitin tarayya na koyon aiki da ke garin Ido ba su kamu da cutar ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng