Sirika: Gudun kamuwa da COVID-19 ta sa na hana Gwamnoni tafiya zuwa ketare

Sirika: Gudun kamuwa da COVID-19 ta sa na hana Gwamnoni tafiya zuwa ketare

A cikin makon nan an samu sama da mutane 100 da aka tabbatar da cewa sun kamu da cutar COVID-19 a Najeriya. Wannan ya sa kasar ta ke cigaba da tsaurara matakan kare jama’a.

Ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika, ya bayyana cewa ya hana wasu gwamnonin jihohi biyar damar barin kasar. Jaridar Daily Trust ta fitar da wannan rahoto a ranar Talata.

Hadi Sirika ya ce bai bada umarni ga jiragen wadannan gwamnoni su bar kasar ba ne domin takaita yaduwar COVID-19.

Sirika ya yi wannan bayani ne a wajen wani taro da aka yi a Abuja.

Mai girma ministan kasar ya shaidawa Duniya cewa biyu daga wadannan gwamnoni da aka hana jirgin samansu tashi daga Najeriya sun fito ne daga yankin kudu maso kudancin Najeriya.

Sirika ya kuma tabbatar da cewa akwai daya daga cikin gwamnonin da ya fito daga Arewa maso arewa watau Arewa ta tsakiya. Ragowar gwamnonin kuma sun fito ne daga kudu maso gabas.

Da ya ke bayani wajen taron da kwamitin PTF mai yaki da cutar COVID-19 wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa, ministan yace akwai ‘yan jam’iyyarsa cikin gwamnonin nan.

KU KARANTA: Za a fara gwajin wani maganin cutar COVID-19 a kasar Birtaniya

Sirika: Gudun kamuwa da COVID-19 ta sa na hana Gwamnonin Jihohi tafiya

Gwamnatin Tarayya ta haramta sauka da tashin jirage a filin jirgin sama
Source: Facebook

Sanata Sirika ya ce uku daga cikin gwamnonin da aka ki ba damar keta hazo, ‘yan jam’iyyar APC mai mulki ne. Hakan na nufin sauran gwamnonin sun fito ne daga jam’iyyun PDP ko APGA.

“Duk wani jirgi da za mu bari ya tashi zai zama tafiyar da ta zama dole ce za ayi, kuma 98% na irin wannan tafiya su na da alaka da annobar cutar Coronavirus.” I

Daidaikun jirage da za su tashi ne su ke na huldar kasa da kasa, ko na daukar mutanen kasar waje, wanda takardunsu ke bi ta hannun ma’aikatar kasar wajen Najeriya.”

“Kafin a bar jirgi ya tashi, sai an bi ke-ke-da-ke, dole a tabbatar tafiyar ta na da matukar muhimmanci ko alaka da kawo magungunan cutar COVID-19 ko kuma shigo da abinci.” Inji ministan na shugaba Buhari.

Ministan harkokin jiragen saman na Najeriya ya ce kafin a dauki wani maras lafiya, dole sai an kawo takardun babban asibiti. Ministan ya roki ayi hakuri da wannan mataki na kariya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel