Yanzu-yanzu: Sabbin Mutane 117 sun kamu da Coronavirus a Najeriya, Legas, Abuja, Kano ke kan gaba
Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutane 117 da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Talata, 19 ga Afrilu, 2020.
Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita inda tace: “An samu karin mutane dari da sha bakwai (17) sun kamu da #COVID19"
59 a Lagos
29 a FCT
14 a Kano
6 a Borno
4 a Katsina
3 a Ogun
1 a Rivers
1 a Bauchi
Kawo karfe 11:25 na daren 21 ga Afrilu, mutane 782 suka kamu da cutar COVID-19 a Najeriya
An sallami: 197
Mutuwa : 25
Mutane biyar da aka ruwaito sun kamu a Legas, an mayar da su jihar Ogun. Saboda haka yanzu Legas mutane 430 take dashi, Ogun kuma 20.
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Sabbin Mutane 117 sun kamu da Coronavirus a Najeriya

Asali: Facebook
Kawo karfe 11:25 na ranar 21 ga Afrilu, ga jerin jihohi da adadin:
Lagos-430
FCT-118
Kano-73
Osun-20
Ogun-20
Oyo-16
Katsina-16
Edo-15
Kwara-9
Kaduna-9
Akwa Ibom-9
Borno-9
Bauchi-8
Gombe-5
Delta-4
Ekiti-4
Ondo-3
Rivers-3
Jigawa-2
Enugu-2
Niger-2
Abia-2
Benue-1
Anambra-1
Sokoto-1
A bangare guda, Sakataran kiwon lafiya kasar Birtaniya, Matt Hancock, ya bayyana cewa an samar da rigakafin cutar COVID-19 kuma ranar Alhamis za'a fara gwadawa kan masu cutar.
Masana ilmin Kimiyan jami'ar Oxford ne suka kirkiri rigakafin mai suna ''ChAdOx1 nCoV-19".
Yayinda yake jawabi a taron da aka shirya a fadar shugaban kasar Ingila, 10 Downing Street, Hancock ya ce gwamnatin na iyakan kokarinta wajen samar da rigakafin cutar COVID-19.
Ya ce gwamnatin ta baiwa masana ilmin Kimiyan jami'ar Oxford Yuro milyan 20 (N.9.5bn) domin taimakawa wajen gwajin rigakafin.
Hancock ya ce za'a kara baiwa wasu masana kimiyan na jami'ar Imperial College dake Landan £22.5 million domin nasu binciken.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng