Sojoji sun yi ma yan bindiga ruwan bamabamai a wani kauyen Neja

Sojoji sun yi ma yan bindiga ruwan bamabamai a wani kauyen Neja

Shelkwatar Sojin Najeriya ta sanar da halaka wasu gungun yan bindiga dadi da dakarun rundunar Sojan sama suka yi a kauyen Maguga cikin karamar hukumar Rafi, jahar Neja.

Daily Trust ta ruwaito shugaban sashin watsa labaru na shelkwatar, Manjo Janar John Enenche ne ya bayyana haka a ranar Talata, inda yace Sojojin suna aikin Operation Gama Aiki ne.

KU KARANTA: Jana’izar Abba Kyari: Jam’iyyar PDP ta nemi a kama sakataren gwamnatin Najeriya

John ya ce rundunar ta kai harin ne a ranar 19 ga watan Afrilu tare da hadin gwiwar dakarun Operation Thunder Strike bayan samun rahoton dandazon yan bindiga tare da dabbobin su.

“Mun samu rahoton an hangi gittawar wasu gungun yan bindiga sanye da bakaken kaya dukansu tare da dabbobin da suka sato a Maguga, nan da nan rundunar Sojin sama ta aika jirgin yaki a kansu, ganin jirgin ke da wuya suka fara boyewa a jikin bishiyoyi.

Sojoji sun yi ma yan bindiga ruwa bamabamai a wani kauyen Neja
Sojoji sun yi ma yan bindiga ruwa bamabamai a wani kauyen Neja
Asali: Twitter

“Amma hakan bai hana jiragen yakin sauke musu ruwan wuta ba, wanda yayi sanadiyyar mutuwar da dama daga cikinsu. Rundunar Sojin Najeriya na gode ma yan Najeriya bisa gudunmuwar da suke bata.

“Haka nan muna kira ga jama’a su cigaba da bamu bayanan sirri ingantattu da zasu taimaka mana wajen yaki da miyagu, tabbatar da tsaro tare da dawo da zama lafiya mai daurewa a kasar.” Inji shi.

A wani labarin kuma, jami’an Yansandan Najeriya reshen jahar Legas sun samu nasarar kama wani kasurgumin dan fashi da makami daya fitini al’ummar yankin Ikorodu na jahar.

Daily Trust ta ruwaito yansanda sun kama Sanni Abiodun inkiya Abbey Boy ne a wani samame da suka kai wata matattarar yan wiwi dake unguwar Ikorodu ta jahar Legas.

Rahotanni sun ce an kama Abiodun ne a mashayar yan wiwin dake titin Araromi dake Igbogbo, inda Yansandan suka binciko wasu makamai tare da buhunan wiwi a wurin.

Bayan shan matsa daga hannun Yansanda, Abiodun ya fallasa maigidansa mai suna Babajide, wanda yace shi ne yake kawo masa tabar wiwin da yake sayarwa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel