Afrika: Jerin Tsofaffi da Jami’an Gwamnati masu-ci da COVID-19 ta hallaka

Afrika: Jerin Tsofaffi da Jami’an Gwamnati masu-ci da COVID-19 ta hallaka

Mummunar cutar nan ta COVID-19 ta kashe fiye da mutane 160, 000 a fadin Duniya daga karshen shekarar bara zuwa yanzu. Ta’adin wannan cuta ya shigo har kasashen Nahiyar Afrika.

Jaridar Daily Trust ta tsakuro wasu daga cikin manya da ake ji da su a Nahiyar da wannan cuta ta kashe. Daga ciki akwai babban hadimin shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari.

1. Abba Kyari (Najeriya)

Malam Abba Kyari ya kasance shugaban ma’aikatar fadar shugaban Najeriya kafin rasuwarsa. Kyari ya rasu ne a ranar 17 ga watan Afrilu, 2020, bayan ya yi fama da jinyar COVID-19.

2. Sékou Kourouma (Guinea)

Sakataren gwamnatin kasar Guinea Sékou Kourouma ya na cikin wadanda wannan cuta ta ga bayansu a Afrika, Kourouma ya na cikin manyan abokan shugaba Alpha Conde na kasar.

3. Jacques Joaquim Yhombi-Opango (Kongo)

Tsohon shugaban kasar Kongo Jacques Joaquim Yhombi-Opango, ya mutu a sakamakon wannan annoba. Joaquim Yhombi-Opango ya cika ne a wani asibitin kasar waje ya na shekara 81.

4. Rose Marie Campoare (Burkina Faso)

COVID-19 ta kashe fitacciyyar ‘yar majalisar Burkina Faso Marie Compaore. Tsohuwar mataimakiyar shugabar majalisar ta na cikin wanda ta fara kamuwa da cutar a Afrika.

5. Victor Traore (Guinea)

A cikin watan nan tsohon darektan hukumar Interpol na kasar Guinea Victor Traore ya cika a wani a asibiti da ke birnin Conakry bayan ya shafe kusan makonni ya na jinyar Coronavirus.

KU KARANTA: Maza sun fi Mata kamuwa da Coronavirus bayan annoba ta leka Jihohi 22

Afrika: Jerin Tsofaffi da Jami’an Gwamnati masu-ci da COVID-19 ta hallaka
Nur Husseini ya mutu a Landan bayan ya kamu da COVID-19
Asali: Facebook

6. Shafie Abdel Halim Dawoud da Khaled Shaltout (Masar)

Coronavirus ta kashe wasu manyan sojojin kasar Masar; Manjo Janar Shafie Abdel Halim Dawoud da Khaled Shaltout. Sojojin su na cikin jami’an da ake ji da su a kasar Masar kafin rasuwarsu.

7. Amadou Salif Kebe (Guinea)

Har wa yau shugaban hukumar zabe na kasar Guinea Amadou Salif Kebe ya rasu a makon da ya wuce a dalilin COVID-19. Salif Kebe ya cika ne a wani asibiti da ke garin Donka a kasar.

8. Mukendi wa Mulumba (DRC)

A watan Maris ne babban jami’in kasar Kongo Jean-Joseph Mukendi wa Mulumba ya rasu a garin Kinsasha. Marigayin ya na cikin masu ba mai girma shugaban kasa Felix Tshisekedi shawara.

9. Kahlif Mumin (Somaliya)

Khalif Mumin ya na cikin wadanda su ka bar Duniya bayan sun yi fama da wannan cuta. Mumin shi ne karamin ministan shari’ar Somaliya kuma babban jami’in gwamnati a Hirshabelle.

Sauran wadanda su ka mutu bayan sun kamu da wannan cuta a Afrika sun hada da tsohon firayim ministan Somaliya Nur Hassan Hussein da tsohon shugaban kasar Libya, Mahmud Jibril.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel