Launin fatar jikin wasu likitocin China ya sauya bayan sun warke daga cutar covid-19

Launin fatar jikin wasu likitocin China ya sauya bayan sun warke daga cutar covid-19

Launin fatar jikin wasu likitocin kasar China guda biyu ya sauya bayan sun sha fama da cutar covid-19.

Farar fatar likocin biyu; Dakta Yi Fan da Dakta Hu Weifen, ta koma launin baki bayan sun warke daga cutar covid-19.

Dakta Fan da Dakta Weifeng; ma su shekara 42 a duniya, sun kamu da kwayar cutar ne a watan Janairu a wani asibiti da ke garin Wuhan, kamar yadda Mail Online ta rawaito.

Likitan da ya duba likitocin biyu ya fada wa gidan talabijin na CCTV da ke kasar China cewa, launin fatar likitocin ya sauya ne saboda illata hantarsu da cutar covid-19 ta yi.

Likitocin biyu abokai ne ga wani likitan kasar China da ya mutu, Li Wenlian, wanda aka hukunta a kan fasa kwai a kan cutar covid-19.

Launin fatar jikin wasu likitocin China ya sauya bayan sun warke daga cutar covid-19

Launin fatar jikin wasu likitocin China ya sauya bayan sun warke daga cutar covid-19
Source: Twitter

Cutar covid-19 ce ta zama sanadiyyar mutuwar Dakta Wenlian a ranar 7 ga watan Fabrairu, 2020.

DUBA WANNAN: Babbar magana: Gwamnatin Legas za ta gurfanar da wasu ma su cutar covid-19

An fara kwantar da likitocin biyu a wani asibitin duba matsalolin da su ka shafi numfashi a Wuhan kafin daga bisani aka mayar da su zuwa wani asibiti da ke Xincheng.

Da ya ke magana da CCTC, Dakta Yi Fan ya bayyana irin mawuyacin halin da ya tsinci kansa yayin da ya ke fama da cutar covid-19.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel