Shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya ya koma bakin aiki bayan ya warke daga coronavirus
- Muhammad Babandede, shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, ya koma bakin aiki
- Sau biyu sakamakon gwaji na nuna shugaban hukumar kula da shige da ficen baya dauke da cutar yan makonni bayan ya killace kansa
- Babandede ya harbu da coronavirus bayan ya dawo daga kasar Birtaniya
Mako guda bayan ya warke daga cutar COVID-19, shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, Muhammad Babandede, ya koma bakin aikinsa.
Hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari a shafukan zumunta, Lauretta Onochie a ranar Talata, 21 ga watan Afrilu, ta bayyana hakan a shafinta na Twitter.
Onochie ta yada hotunan Babandede a yayinda ya koma bakin aikin nasa a hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, a ranar Litinin, 20 ga watan Afrilu.
KU KARANTA KUMA: A yi ma na afuwa: Mun yi kuskure a wajen binne Abba Kyari - PTF
Ku tuna cewa Babandede ya kamu da cutar COVID-19 a watan Maris sannan ya shiga killace kansa tun bayan da ya dawo daga kasar Birtaniya.
Sai dai ya warke biyo bayan gwaji da aka yi masa sau biyu a inda yake killace, inda dukka sakamakon suka nuna baya dauke da cutar kuma.
Kakakin hukumar kula da shige da fice ta kasar, Sunday James, ne ya bayyana batun warkewar nasa a cikin wata sanarwa a ranar Talata, 15 ga watan Afrilu a Abuja.
Har ila yau Babandede ya gode wa mutanen da suka yi ta yi masa addu'a har ya samu sauki daga cutar ta COVID-19.
Shima da kansa a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Babandede ya ce sakamako na biyu na gwajin da aka yi masa ya nuna cewa ya warke daga cutar.
A wani labarin kuma, Shugaban kungiyar likitocin Najeriya, NMA, reshen jahar Sakkwato, Dakta Sani Abubakar ya sanar da kamuwarsa da annobar Coronavirus kamar yadda sakamakon gwaji ya tabbatar.
Daily Trust ta ruwaito cewa Sani Abubakar ne mutumin da gwamnan jahar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana ma al’ummar jahar kamuwarsa da cutar, sai dai bai bayyana sunansa ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng