Kaso 90 na wadanda suka kamu da coronavirus za su warke - Minista

Kaso 90 na wadanda suka kamu da coronavirus za su warke - Minista

Ministan lafiya, Osagie Ehanire, ya ce kaso 90 cikin 100 na mutanen da suka kamu da cutar coronavirus, za su warke daga cutar.

Mista Ehanire yayinda ya ke amsa tambayoyi a taron kwamitin shugaban kasa na PTF a ranar Litinin, 20 ga watan Afrilu, ya ce mutane sun tsorata da cutar.

Ya ce hakan ya kasance sakamakon yawan adadin mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar, “wanda hakan ya sa suke mantawa da yawan wadanda suka warke.”

“Motar daukar marasa lafiya na iya aiwatar abubuwa da dama, don haka alamar motar asibiti baya fassara COVID-19 a take. Sai dai hakan na haifar da tsoro.

“Yana iya afkuwa amma a wannan lamari, ban yarda da haka ba. Babu dalilin fargaba saboda kaso sama da 90 cikin 100 na wadanda suka kamu da COVID-19 za su warke.

“Mutane tara cikin 10 za su warke, don haka menene abun tsoro a ciki. Kawai dai adadin na da yawa wanda hakan ya sa muka manta cewa mutane na warkewa kuma yan kadan ne ke shiga halin tsananin rashin lafiya, wannan kimanin hudu zuwa biyar cikin 100,” in ji Mista Ehanire.

Kaso 90 na wadanda suka kamu da coronavirus za su warke - Minista

Kaso 90 na wadanda suka kamu da coronavirus za su warke - Minista
Source: UGC

A safiyar ranar Talata, Najeriya ta samu yawan mutane 665 da suka kamu da COVID-19, cikin su 188 sun warke kuma an sallame su yayinda 22 suka mutu, jaridar Premium Times ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya ya koma bakin aiki bayan ya warke daga coronavirus

Wasu daga cikin mutanen da suka mutu sakamakon cutar a Najeriya dama suna da wasu cututtukan.

Kimanin mutane miliyan biyu ne suka kamu da COVID-19 a duniya, 169,940 sun mutu, sannan 645,164 sun warke.

A wani labarin, Shugaban kungiyar likitocin Najeriya, NMA, reshen jahar Sakkwato, Dakta Sani Abubakar ya sanar da kamuwarsa da annobar Coronavirus kamar yadda sakamakon gwaji ya tabbatar.

Daily Trust ta ruwaito cewa Sani Abubakar ne mutumin da gwamnan jahar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana ma al’ummar jahar kamuwarsa da cutar, sai dai bai bayyana sunansa ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel