A yi ma na afuwa: Mun yi kuskure a wajen binne Abba Kyari - PTF

A yi ma na afuwa: Mun yi kuskure a wajen binne Abba Kyari - PTF

Kwamitin fadar shugaban kasa a kan COVID-19, ta bayar da hakuri a kan wasu kura-kurai da aka yi, a lokacin binne marigayi shugaban ma’aikatan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Abba Kyari.

An binne Kyari, wanda ya rasu a ranar Juma’a sakamakon annobar coronavirus, a makabartar Gudu da ke Abuja a ranar Asabar.

Yan Najeriya da dama, musamman a shafukan soshiyal midiya, suna ta korafin cewa mafi akasarin wadanda suka halarci jana’izar basu bi umurnin jan tazara a tsakani ba da matakan kariya da ya kamata.

Amma a jawabinsa a ranar Litinin, 21 ga watan Afrilu, Shugaban tawagar na kasa, Sani Aliyu, ya ce kamata ya yi a lura da dandazon jama’ar.

A yi ma na afuwa: Mun yi kuskure a wajen binne Abba Kyari - PTF

A yi ma na afuwa: Mun yi kuskure a wajen binne Abba Kyari - PTF
Source: Twitter

“Tawagar PTF na bayar da hakuri a kan kurakuran da aka yi a lokacin binne marigayi Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa,” in ji PTF din.

“Mun gano cewa ba a daidaita taron jama’ar ba, mun koyi darasi daga wannan kuma za mu tabbatar da hakan bai sake faruwa a gaba ba za a kiyaye tare da bin tsarin kwamitin.

“Tuni aka tsaftace makabartar Gudu, an yiwa kayayyakin kariyar da aka watsar a wajen feshi, sannan aka kona su tare da zubar dasu daidai da tsarin NCDC.

“Zan so yin karin haske kan batun COVID-19 da tsarin binne wanda ya mutu. Sabanin abunda ya ke a soshiyal midiya, an shirya gawar marigayi Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa a tsanaki domin binnewa, bisa ga tsarin NCDC da koyarwar addinin Musulunci.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Gwamna Zulum ya rufe jahar Borno na tsawon kwanaki 14

“Kamar yadda WHO ta bayyana a tsarinta, gawar mutumin da ke dauke da COVID-19 bata harban wani. Har yanzu babu wani hujja da ke nuna cewa mutum zai kamu da cutar don ya hadu da gawar wanda ya mutu sakamakon COVID-19.”

Kwamitin ya ce zai ci gaba da bin tsari da sharudan NCDC wajen binne wanda ke da COVID-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel