Covid-19: Yadda dandazon jama'a ke hada-hada a kasuwannin FCT

Covid-19: Yadda dandazon jama'a ke hada-hada a kasuwannin FCT

A jiya an ga mutane masu tarin yawa a kasuwannin birnin tarayya suna karya dokar gwamnatin tarayya.

Jaridar Daily Trust ta lura cewa an karya dokokin nisantar juna a kasuwannin Garki, Wuse, Nyanya da Karu.

'Yan kasuwa da masu siyayya sun take dokar nisantar juna inda suke ta hada-hadarsu.

Ministan babban birnin tarayya, Muhammad Musa Bello ya rage kwanakin zuwa kasuwa inda ya mayar da su kwanaki biyu kacal a cikin mako.

Hatta direbobi a kan manyan tituna sun take dokar da gwamnatin ta saka na daukar jama'a kadan a cikin motocin haya.

Amma kuma, wasu daga cikin kasuwannin sun bi wasu daga cikin ka'idojin don an tilasta jama'a saka takunkumin fuska kafin shiga.

Eugenia Andrew na tafe da sinadarin kashe kwayoyin cuta kuma tana amfani da shi lokaci zuwa lokaci ballantana idan ta taba kayayyaki a kasuwa.

Ta ce taron jama'a bai yawaita a kasuwa ba kuma an kiyaye dokar nisanta juna. Cunkoso ya fi yawa a bangaren masu siyar da kayan abinci.

Covid-19: Yadda dandazon jama'a ke hada-hada a kasuwannin FCT

Covid-19: Yadda dandazon jama'a ke hada-hada a kasuwannin FCT
Source: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: An dakatar da gwajin Covid-19 a jihar Kano

Wasu kwastomomi sun nuna damuwarsu a kan dandazon jama'a da suka cika kasuwa sannan sun yi kira ga gwamnati da ta dauka matakan tsaftace kasuwar.

Wani mai siyar da kifi a kasuwar Karu, Rabi'atu Adewale, ta ce: "Tunda ba za a iya rufe kasuwar dukkanta ba, ya kamata gwamnati ta samu hanyoyin wayar da kai ga jama'a da ke cikin cunkoso. Cunkoson ya yi yawa amma dole ce ta sa muka fito."

Wani mai siyayya mai suna Mamman Hassan ya ce "Lokacin da na iso kasuwar a yau, na sha mamaki da na ga cunkoson jama'a.

"Muna ta mu'amala babu takunkumin fuska, sinadarin kashe kwayoyin cuta ko kiyaye dokokin nisantar juna. A gaskiya akwai bukatar daukar mataki."

Wani mai shago a kasuwar Wuse mai suna Mohammed Sale, ya ce bai damu koda jama'a basu kiyaye dokar nisantar juna a shagonsa ba.

"Na yi kwanaki a gida amma yanzu na samu damar samun kudi ba zan takura kwastomomi ba," a cewarsa.

Shugaban kawamitin yaki da cutar coronavirus na birnin tarayyar, Ikharo Attah, ya ce an samu cunkoson ne sakamakon rubibin siyayyar kayan azumi da kuma tsoron rufe jama'a babu kayan abinci.

Kamar yadda yace, da yawa daga cikin kwastomomin da ke kasuwar musulmai ne masu bukatar yin siyayyar azumi.

Attah ya ce, ya zagaya kasuwanni da amsa-kuwwa inda yake tunatar da jama'a amfanin nisantar juna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel