Yanzu-yanzu: Wanda ya debo Coronavirus daga Indiya ya mutu a Legas

Yanzu-yanzu: Wanda ya debo Coronavirus daga Indiya ya mutu a Legas

Wani dan shekara 45 wanda ya dawo Najeriya daga kasar Indiya ya kwanta dama a jihar Legas bayan fama da cutar Coronavirus na tsawon makonni.

Kwamishanan kiwon lafiyan jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita ranar Talata.

Yace, “Ba a samu ko mutum daya da ya kamu da COVID-19 ranar 20 ga Afrlu, 2020 a jihar Legas ba amma an samu wadanda suka mutu sakamakon cutar a Legas.“

“Daya daga cikin wadanda ya mutu wani namiji ne mai shekaru 45 da haihuwa wanda ya dawo daga kasar Indiya a watan Jumairu, 2020.“

“Na biyun kuma wata budurwa ce yar Najeriya, mai shekaru 36 a duniya wacce ta kasance mai fama da wasu cututtuka kafin Coronavirus.“

“Yanzu jimillan wadanda suka mutu a jihar Legas 16 ne.“

Yanzu-yanzu: Wanda ya debo Coronavirus daga Indiya ya mutu a Legas
Kwamishnan Lafiyan Legas
Asali: Twitter

KU KARANTA Gwamnati ta rufe asibitin da Abba Kyari ya mutu a Legas

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutane 38 da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Lahadi, 19 ga Afrilu, 2020.

Kawo daren Litinin, mutane 665 suka kamu da cutar, 188 sun warke kuma 22 sun mutu.

An samu bullar cutar Coronavirus a Sakkwaton Shehu, Gwamnatin jihar ta tabbatar.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana hakan ne a jawabin da yayiwa manema labarai da daren Litinin, 20 ga watan Afrilu, 2020.

A cewarsa, mutumin da ya kamu na kwance a asibitin koyarwan jami'ar Usamanu DanFodio, dake jihar.

Yace: "Ya ku al'ummar jihar Sokoto, cikin bakin ciki nike ina mai sanar muku da labaran cewa an samu bullar annobar Coronavirus a nan jihar Sokoto."

"Tunda an tabbatar da kamuwar mutumin, za'a kai shi cibiyar killacewa dake Amanawa."

"Ina kira ga al'ummar jiharmu da su cigaba da biyayya ga shawarin da jami'an kiwon lafiya suka bada domin takaita yaduwar cutar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel