Babban magana: Shugaban likitocin jahar Sakkwato ya kamu da Coronavirus
Shugaban kungiyar likitocin Najeriya, NMA, reshen jahar Sakkwato, Dakta Sani Abubakar ya sanar da kamuwarsa da annobar Coronavirus kamar yadda sakamakon gwaji ya tabbatar.
Daily Trust ta ruwaito cewa Sani Abubakar ne mutumin da gwamnan jahar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana ma al’ummar jahar kamuwarsa da cutar, sai dai bai bayyana sunansa ba.
KU KARANTA: Mayakan Boko Haram sun yi awon gaba da mace mai ciki da yaronta a jahar Yobe
Dakta Sani da kansa ya sanar da kamuwa da cutar a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook a ranar Litinin inda yace:
“Sakamakon gwaji ya nuna ina dauke da cutar Coronavirus. A yanzu haka na fara samun kulawa, kuma babu wata matsala a tare da ni a yanzu.
“Ban yi tafiya zuwa ko ina ba, kuma ban yi mu’amala da wani mai dauke da cutar ba, amma tun da aka tabbatar da cutar a kai na, sai na killace daga iyalai na da abokai na. kwamitin yaki da COVID-19 na jahar Sakkwato ta na aikinta kamar yadda doka ta tanada.
“Daga karshe ina kira ga abokaina su sani cewa an kai matsayin yaduwar cutar a tsakanin jama’a, don haka jama’a mu lura, kuma mu tabbata mun bi ka’idojin da aka shimfida na kare kai domin mu zauna laifya.” Inji shi.
Da yake sanar da samun bullar cutar a karon farko a jahar Sakkwato, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya ce:
“Innalillahi wa Inna Ilaihi raji’un! Jama’an jahar Sakkwato, tare da alhini da damuwa nake sanar da ku cewa annobar COVID-19, ma’anan Coronavirus ta shigo jahar Sakkwato.
“A yanzu haka mun fara shirin killace mutumin a wurin killacewa dake Amanawa. Ina kira ga jama’a su cigaba da bin ka’idojin da aka shimfida don kare yaduwar cutar nan,.
"Muna jin sa ne a baya, amma a yanzu ya shigo cikinmu, don haka ya kamata mu zage damtse domin kare yaduwarsa.” Inji shi.
A wani labarin kuma, An samu karin mutane 23 a jahar Kano da suka kamu da annobar nan mai toshe numfashi, watau Coronavirus, hakan ya kawo adadin masu cutar a Kano zuwa 59.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng