Jami’an Yansanda sun kama kasurgumin Dan fashi a matattarar yan wiwi

Jami’an Yansanda sun kama kasurgumin Dan fashi a matattarar yan wiwi

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Legas sun samu nasarar kama wani kasurgumin dan fashi da makami daya fitini al’ummar yankin Ikorodu na jahar.

Daily Trust ta ruwaito yansanda sun kama Sanni Abiodun mai inkiya da ’Abbey Boy’ ne a wani samame da suka kai wata matattarar yan wiwi dake unguwar Ikorodu ta jahar Legas.

KU KARANTA: Annobar Corona: Gwamna ya fara biyan matasan jaharsa N30,000 a Najeriya

Rahotanni sun ce an kama Abiodun ne a mashayar yan wiwin dake titin Araromi dake Igbogbo, inda Yansandan suka binciko wasu makamai tare da buhunan wiwi a wurin.

Mataimakin sufetan Yansandan shiyya ta 2, AIG Ahmed Iliyasu ne ya bayyana haka yayin da yake bajekolin dan fashin a babban ofishin Yansandan shiyyar.

Jami’an Yansanda sun kama kasurgumin Dan fashi a matattarar yan wiwi
Jami’an Yansanda sun kama kasurgumin Dan fashi a matattarar yan wiwi
Asali: Facebook

Iliyasu yace sun kai samamen ne bayan samun koke-koken jama’a game da miyagun ayyukan Abbey da yaransa a yankin, don haka ya umarci hazikin Dansanda, Uba Adams ya kamo shi.

AIG Iliyasu yace bayan sun yi ma Abbey tambayoyi, ya amsa laifinsa, kuma ya tabbatar da mallakar bindigar da aka gani a wajensa da alburusai, wanda yace da su yake amfani a fashi.

Da ya sha matsa, Abbey ya bayyana sunan wani mutumi Babajide a matsayin maigidansu, wanda yace shi ne ya kawo masa tabar wiwin da aka kama domin ya sayar masa.

Daga karshe, Iliyasu yace tuni sun kaddamar da farautar Babajide don tabbatar da sun kama shi, sa’annan yace zasu gurfanar da Abbey gaban kotu da zarar sun kammala bincike a kansa.

A wani labarin kuma, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnati ba za ta lamunci harin da yan bindiga suke kai a jahar Katsina ba, don haka ya yi alkawarin daukan mataki.

Daily Trust ta ruwaito Buhari ya bayyana haka ne biyo bayan mummunan harin da yan bindiga suka kai a kananan hukumomi uku, inda suka kashe mutane 47, tare da jikkata wasu da dama.

Buhari ta bakin kakaakakinsa, Garba Shehu ya ce ba za su bari harin ya wuce haka nan ba har sai sun rama biki da harin ramuwar gayya, wanda yayi daidai da tsarinsa na kare jama’an kasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng