Dokar hana fita: Rikici ya barke a Jigawa bayan an harbi yaro mai shekara 10

Dokar hana fita: Rikici ya barke a Jigawa bayan an harbi yaro mai shekara 10

Wani kazamin rikici ya barke a kauyen Sankara da ke karkashin karamar hukumar Ringim a jihar Jigawa bayan an zargi jami'an 'yan sanda da harbin wani yaro mai shekaru goma.

Mazauna kauyen sun yi zargin cewa jami'an 'yan sanda sun harba bindiga da barkonon tsohuwa domin tarwatsa jama'ar da ke cin kasuwar garin Sankara ranar Litinin.

Ana zargin cewa daya daga cikin alburusan da 'yan sandan su ka harba ne ya samu yaron mai suna Usman Abdulkadir.

A kwanakin baya ne gwamnatin Jigawa ta sanar da dakatar da cin kasuwanni sati - sati a jihar domin dakile yaduwar annobar cutar covid-19.

Jami'an 'yan sanda sun dira a kasuwar ne domin tabbatar da dokar hana cin kasuwanni ta yi aiki.

Mahaifin yaron, Abdulkadir Usman, ya shaidawa jaridar Premium Times cewa harsashin bindiga ya runata dansa.

Dokar hana fita: Rikici ya barke a Jigawa bayann dan sanda ya harbi yaro mai shekara 10

Rikici ya barke a Jigawa bayan dan sanda ya harbi yaro mai shekara 10
Source: Twitter

A cewar Abdulkadir, an fara kai Usman asibitin garin Sankara kafin daga bisani aka mayar da shi zuwa babban asibitin garin Ringim.

"Ana kokarin ceton ransa, amma ba ya cikin hayyacinsa.

DUBA WANNAN: Covid-19: 'Yan KAROTA sun kama mutane 350, motoci 35 a Kano

"Duk mun san dan sandan da ya harbe shi, kowa ya san irin muguntarsa" a cewar mahaifin yaron.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Jigawa, Audu Jinjiri, ya ce jami'an 'yan sanda sun je kasuwar ne domin tabbatar da dokar kulle, amma sai su ka fuskanci tirjiya daga wurin jama'a.

Jinjiri ya bayyana cewa jama'ar da ke kasuwar sun rufe 'yan sanda da jifa da duwatsu.

Sai dai, kakakin ya musanta cewa harsashi ne ya raunata yaron a ka.

"Daya daga cikin irin duwatsun da fusatattun jama'a ke jifa dasu ne ya same shi," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel