Darajar gangar danyen man Amurka ta sauka zuwa dala $0.1 a kasuwannin duniya
Farashin gangar danyen mai na kasar Amurka ya yi saukan da bai taba yi ba a shekara 22 a ranar Litinin inda ya karye da kashi 40 zuwa dala $0.1 sakamakon annobar Coronavirus.
Rahoton kamfanin dillancin labaru na AFP yace tun shekarar 1998 rabon da a samu irin wannan karyewa warwas da farashin gangan danyen mai ya yi a wannan lokaci.
KU KARANTA: Hukumar KEDC ta dakatar da yanke wutar lantarki a jahar Kaduna saboda Corona
Wani masanin kasuwancin man fetir, Bjornar Tonhaugen ya bayyana dalilin wannan lamari shi ne kasancewar kasashe da dama suna da tarin man fetir a kasa don haka basa bukatar kari.
Masanin yace a yanzu haka ba’a amfani da man fetir saboda duniyar ta tsaya cak a dalilin annobar Corona, tun da ba’a amfani da mai, babu bukatar saye, saboda haka mai ya yawaita.
Duk kuwa da matakin da kungiyar kasashe masu arzikin man fetir, OPEC, ta dauka na rage gangan mai miliyan 10 daga danyen man da ake fitarwa a duk rana, sai da farashin ya karye.
Idan za’a tuna a kwanakin baya ne gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta rage farashin litar man fetir sakamakon karyewar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.
Gwamnatin ta tsara kasafin kudin shekarar 2020 a kan hasashen farashin gangar danyen mai ba zai yi kasa da $30 ba, saboda shi ne kadai hanyar samun kudin shiga mafi girma a wajenta.
A yanzu da farashin danyen man na Amurka ya karye zuwa $0.1, sai dai a zura idanu a ga yadda gwamnatin kasar Amurka za ta shawo kan matsalolin tattalin arzikin kasar da zasu biyo.
A wani labarin, Tsohon minista a jamhuriya ta biyu, Alhaji Sama’ila Isah Funtua ya shawarci masu danganta shi da mukamin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa da su kai kasuwa.
Funtua, ya taba zama jami’in mulki a Katsina na tsawon shekaru 7, ministan ruwa, kuma yana cikin mutanen da suka tsara daftarin kundin tsarin mulki a shekarar 1994-1995.
Don haka ya ce baya bukatar wannan mukami saboda a cewarsa shi kan sa yana daukan mutane aiki a Najeriya, don haka ya girmi wani ya dauke shi aiki a wannan lokaci.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng