Yanzu-yanzu: Kwankwaso ya bada gudunmuwar sabuwar asibitinsa don yakar Coronavirus

Yanzu-yanzu: Kwankwaso ya bada gudunmuwar sabuwar asibitinsa don yakar Coronavirus

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a ranar Litinin ya bada gudunmuwar sabuwar asibitinsa ta Amana Hospital ga gwamnatin jihar domin yakar COVID-19.

Kakakin Kwankwaso, Saifullahi Hassan, ya bayyana cewa Sanata Kwankwaso ya bada gudunmuwar ne ga kwamitin ko-ta-kwanar yakin ciyar Coronavirus a jihar.

Saifullahi Hassan ya ce“ Amana Hospitial sabuwar asibiti ce mai sabbin gadaje 60.“

“An kammala ginata watan da ya gabata kuma ko kaddamar da ita ba a yi ba. Tana Miller Road, Bompai, Kano.”

Jihar Kano ce ta uku a jerin jihohi masu yawan adadin masu cutar Coronavirus a fadin tarayya.

Bayan kwanaki 9 da bullatar cutar a jihar, yanzu an samu mutane 36 da suka kamu da cutar kuma daya ya mutu.

Duk da dokar ta bacin da aka sanya na tsawon mako daya a jihar, bidiyo ta bayyana kan yadda wasu matasa suka shirya gasar kwallo tare da masu kallo zagaye da su.

Har yanzu gwamnatin jihar ba tayi tsokaci kan bidiyon dake yaduwa ba.

KU KARANTA An sake sallamar mutum na 7 daga asibiti bayan samun waraka daga Coronavirus

Yanzu-yanzu: Kwankwaso ya bada gudunmuwar sabuwar asibitinsa don yakar Coronavirus
asibitinsa don yakar Coronavirus
Asali: Facebook

Yanzu-yanzu: Kwankwaso ya bada gudunmuwar sabuwar asibitinsa don yakar Coronavirus
Yanzu-yanzu: Kwankwaso ya bada gudunmuwar sabuwar asibitinsa don yakar Coronavirus
Asali: Facebook

Majalisar dinkin duniya (UN) ta ce ma'aikacinta da cutar covid-19 ta hallaka a jihar Borno bashi da tarihin yin bulaguro zuwa wajen jihar Borno.

Edward Kallon, jagoran harkokin aiyukan taimako na UN a Najeriya, ya ce su na kokarin bin sahun duk mutanen da marigayin ya yi mu'amala da su kafin mutuwarsa.

A ranar Lahadi ne rahotanni su ka bayyana cewa wani ma'aikacin UN ya mutu a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri bayan an kwantar da shi sakamakon nuna alamomin rashin lafiya irin na cutar covid-19.

"Marigayin ya sadaukar da rayuwarsa ne wajen taimakon mutanen da ke zaune a sansanin 'yan gudun hijira."

"Bashi da tarihin yin bulaguro zuwa wajen jihar Borno."

Hakazalika an samu bullar cutar na biyu a jihar Jigawa bayan mutum na farko da jihar Kano ta mayarwa makwabciyarta.

Yanzu jihar Kebbi, Sakkwato da Zamfara kadai suka rage a yankin Arewa maso yamma da basu samu bullar cutar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel