COVID-19: Gwamnatin Kano ta musanta jita jitan mutuwar mutane birjik a Kano

COVID-19: Gwamnatin Kano ta musanta jita jitan mutuwar mutane birjik a Kano

- Gwamnatin Kano ta karyata rade-radin da ke yawo kan cewa mutane na mutuwa birjik a jahar a yan kwanakin nan

- Ta bayyana hakan a matsayin ayyukan masu yada zantuka mara tushe da na kafofin labarai

- Ma'aikatar lafiya ta jahar ta ce babu makawa tana ganin haske a yaki da take yi da COVID-19 a jahar

Gwamnatin Kano ta yi watsi da rade-radin da ke yawo kan cewa mutane na mutuwa birjik a jahar a yan kwanakin nan.

A wani rabutu da ma’aikatar jinya ta jahar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta bayyana cewa babu gaskiya a cikin jita-jitan. Ta bayyana hakan a matsayin aikin masu yada zantuka marasa tushe.

Ma’aikatar lafiyar ta jaddada cewa tana daukar matakai da suka kamata domin ganin ta dakile annobar COVID-19 a jahar. Ta kuma ce tana da karfin gwiwa a kan yaki da take yi da annobar.

COVID-19: Gwamnatin Kano ta musanta jita jitan mutuwar mutane birjik a Kano

COVID-19: Gwamnatin Kano ta musanta jita jitan mutuwar mutane birjik a Kano
Source: Twitter

Ga cikakken jawabin da ta wallafa a shafin nata:

"Sanarwa!!! Game da rade-radin da ke yawo a kan yawan mutuwa da ake yi a jahar Kano.

"Ku yi watsi da jita-jitan samun yawan mace-mace a Kano a yan kwanakin nan. Tawagar jahar kan COVID-19 ta samar da masu kawo mata rahoto na gari-gari, a bisa tsarin hukumar lafiya ta duniya.

"An tanadi mutanen da za su kai rahoton mutuwa da sanadin mutuwar, sannan kuma an zuba jami’ai a dukkanin makabartu domin su kirga yawan gawawwakin da ake binnewa a kullun (ma’aikatan za su yi aiki a rukuni biyu).

"Gaskiyar magana masu yada jita-jita a kafofin labarai na ta kokarin ganin sun wahalar damu wajen wancakalar dasu. An yi bincike a kan wannan zargi kuma an gano ba gaskiya bane, don haka ya zama dole na yi watsi dashi.

"Muna rokon ku mabiya da ku taimaka wajen fayyace gaskiyar lamari. Ba za mu so ganin mutanen Kano sun tashi hankulansu ko yanke kauna daga yadda muke tafiyar da lamarin ba.

KU KARANTA KUMA: An samu muhimman bayanai a kan mutumin da cutar covid-19 ta kashe a jihar Borno

"Ya zama dole mu sanar da cewa muna da karfin gwiwa sosai a yaki da muke da wannan annoba."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng News

Online view pixel