Jerin kasashen da suka fi kamu wa da cutar coronavirus a nahiyyar Afirka - WHO

Jerin kasashen da suka fi kamu wa da cutar coronavirus a nahiyyar Afirka - WHO

- Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce an samu akalla mutane 21,000 da suka kamu da cutar coronavirus a nahiyyar Afirka

- Hukumar ta ce an samu mutane 5000 da suka warke daga cutar yayin da ta kashe mutane 1000 a nahiyyar

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce fiye da mutane 21,000 sun kamu da cutar coronavirus a nahiyar Afirka.

A yayin da mutane 5000 suka warke daga cutar, an kuma samu mutum 1000 da cutar ta yi sanadiyar mutuwarsu kamar yadda hukumar ta bayyana.

A wata sabuwar wallafar alkalumma da hukumar ta fitar a ranar Litinin, 20 ga watan Afrilun 2020, ta nuna jerin kasashen da cutar ta fi harbi a nahiyyar Afirka.

Cikin jerantan, WHO ta nuna cewar akwai mutane 541 da cutar ta harba a Najeriya, wanda hakan na nufin hukumar ta kididdigar alkalummanta ne gabanin cibiyar dakile yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta fidda nata.

A sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.50 na daren ranar Lahadi, 19 ga watan Afrilu, adadin wadanda cutar coronavirus ta harba a kasar ya kai 627.

Alkalumman WHO sun tabbatar da cewa an samu mutane 3,158 da annobar ta harba, 2,629 a Algeria, 1,042 a Ghana yayin da 1,016 suka harbu a kasar Kamaru.

Dubi alkalumman da WHO ta fitar:

Jerin kasashen da suka fi kamu wa da cutar coronavirus a Afirka - WHO
Jerin kasashen da suka fi kamu wa da cutar coronavirus a Afirka - WHO
Asali: UGC

A ranar Lahadi ne hukumomin kasar Saudiya suka tabbatar da karin mutum 1,088 da suka kamu da cutar corona, inda jimillar masu dauke da cutar a kasar ya doshi 10,000.

KARANTA KUMA: Har yanzu ko a Najeriya ba a samu allurar riga-kafin cutar coronavirus ba - WHO

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito ma'aikatar lafiyar kasar yayin da ta ke bayar da shaidar adadin mutane 9,362 da cutar corona ta harba, lamarin da ta ce adadin zai ci gaba da karuwa.

Kamar yadda kamfanin dillancin labaran Saudiya SPA ya ruwaito daga mai magana da yawun ma'aikatar lafiyar kasar, Dr. Muhammad Al-Abdel yana cewa cikin sa'a 24 an samu karin mutum biyar da suka mutu a sanadiyar annobar corona.

Ya tabbatar da cewa ya zuwa yanzu mutane 97 kenan cutar corona ta kashe a Saudiya.

Sai dai ya ce wadanda mai yankan kauna ta riska a baya-bayan nan ba asalin 'yan kasar bane illa iyaka mazaunanta da suka kunshi mutum hudu a Makkah da kuma daya a Jeddah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: