Gwamna Badaru ya bayyana yadda annobar covid-19 ta shiga jiharsa a karon farko

Gwamna Badaru ya bayyana yadda annobar covid-19 ta shiga jiharsa a karon farko

A ranar Lahadi ne gwamnan jihar Jigawa, Mohammed Badaru Abubakar, ya yi karin bayani a kan tabbatar da samun bullar annobar cutar covid-19 a jiharsa a karon farko.

A daren ranar Lahadi ne cibiyar kula da cututtuka ma su yaduwa ta kasa (NCDC) ta fitar da sanarwar cewa annobar ta bulla jihar Jigawa yayin sanar da karin mutane 86 da su ka kamu da kwayar cutar a Najeriya.

Sai dai, NCDC ba ta bayar da karin bayani a kan mutumin da aka samu ya na dauke da kwayar cutar ba a jihar Jigawa.

A wata ganawa da ya yi da manema labarai ranar Lahadi, gwamna Badaru ya yi karin haske a kan mutumin da aka tabbatar ya na dauke da kwayar cutar a jiharsa.

Badaru ya bayyana cewa mutumin da aka tabbatar ya na dauke da kwayar cutar, dan kasuwa ne da ke fita fatauci zuwa kudancin Najeriya daga karamar hukumar Kazaure.

Mutumin, wanda keda shagon sayar da sutura, ya fara nuna alamomin kwayar cutar covid-19 bayan dawowarsa daga kudancin Najeriya, kamar yadda ya saba fita harkokinsa na kasuwanci, a cewar Badaru.

Gwamna Badaru ya bayyana yadda annobar covid-19 ta shiga jiharsa a karon farko
Gwamna Badaru
Asali: Depositphotos

Gwamnan ya kara da cewa mutumin ya ziyarci jihohi da dama kafin ya fara nuna alamomin rashin lafiya.

A cewar gwamnan Badaru, gwamnatin Jigawa ta tuntubi jihohin da mutumin ya ziyarta tare da ba su muhimman bayanai da za su bawa jihohin damar zakulo mutanen da ya yi mu'amala da su.

DUBA WANNAN: Murnar mutuwar Kyari: Kwamishinan da Ganduje ya tube ya yi magana a karo na farko

Badaru ya bayyana cewa yanzu haka an mayar da mutumin zuwa cibiyar killacewa da ke garin Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Gwamnan ya bukaci mutanen jihar Jigawa su kwantar da hankulansu tare da ba su shawarar su cigaba da biyayya da matakan kare kai da dakile yaduwar annobar covid-19.

Kazalika, ya bayar da umarnin kulle karamar hukumar Kazaure domin cigaba da bincike da kuma dakile yaduwar annobar covid-19 a jihar Jigawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel