Har yanzu ko a Najeriya ba a samu allurar riga-kafin cutar coronavirus ba - WHO

Har yanzu ko a Najeriya ba a samu allurar riga-kafin cutar coronavirus ba - WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta jaddada cewa har yanzu babu wata allurar riga-kafin cutar coronavirus da aka samu a ko ina a Najeriya da ma nahiyyar Afirka baki daya.

Sai dai hukumar a sanarwar da ta fitar a ranar Litinin ta ce ana ci gaba da lalube tukuru domin gano maganin cutar da ta zame wa duniya alakakai.

Shugabar cibiyar allurar riga-kafi ta Hukumar Lafiyar reshen Najeriya, Dakta Fiona Braka, ita ce ta bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito Dr. Braka yayin da ta ke bayyana kwazon da mahukuntan lafiya na duniya ke yi babu dare babu rana domin gano riga-kafin cutar.

Dakta Braka ta ce kasancewar cutar covid-19 sabuwar cuta, har yanzu ba a samu riga-kafinta ba, illa iyaka mahukuntan lafiya na bakin kokarinsu wajen wayar da kan al'umma a kan hanyoyin kare kai daga kamuwa da cutar.

Cikin kalamanta, "COVID-19 sabuwar cuta ce da ya zuwa yanzu haka babu wata allurar riga-kafin ta da aka samu wadda za ta iya magance annobar da ta yiwa duniya kawanya."

Shugaban WHO; Tedros Adhanom Ghebreyesus
Shugaban WHO; Tedros Adhanom Ghebreyesus
Asali: UGC

"Babu shakka masana kimiyya na ci gaba da gudanar da ayyukan bincike tukuru domin gano maganin ta."

"Sai dai irin wannan bincike na daukan lokaci mai tsayi domin tabbatar an samu karbabben magani gama gari kuma wanda zai yi tasiri wajen kawar da annobar."

Ta ke cewa, "a iyaka sanin Hukumar Lafiya ta Duniya, babu kamshin gaskiya a rade-radin da ke yaduwa kan cewa an samu maganin cutar covid-19."

KARANTA KUMA: Ya kamata gwamnati tayi bincike a kan mutuwar Abba Kyari - Falana

Bugu da kari "WHO ba ta da masaniyar samun allurar riga-kafin Covid-19 a Najeriya."

"Akwai babban binciken kimiyya da gwaje-gwajen asibiti da ake gudanarwa a yanzu cikin ƙasashe da dama a kan nazarin tasirin wasu magunguna domin magance coronavirus."

"Sakamakon wannan gwaje-gwaje zai taimaka wajen fahimtar ingancin wadannan magungunan kuma zai yi tasiri ta fuskar sake duba ka'idodin kula da wadanda cutar ta harba," inji Braka.

Dangane da yunkurin dakile yaduwar cutar Covid-19, Braka ta ce gwamnatin Najeriya tare da hadin gwiwar cibiyar kula da yaduwar cututtuka a kasar na ci gaba da taka rawar gani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel