Coronavirus ta kawo tsaiko a shari’u 155,757 a Najeriya
An nuna damuwa kan tsaikon da aka samu wajen gudanar da shari’un kotu guda 155,757, a wannan shekarar sakamakon dokar hana fita da aka sanya, domin dakile yaduwar annobar COVID-19 a Najeriya.
Hakazalika, ci gaba da shari’an mutane 51,983 da ke jiran hukunci a hukumar gyara halayya ta Najeriya ya hadu da cikas, wanda hakan zai tsawaita lokacin da za su dauka a tsare.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 29 ga watan Maris, ya sanar da hana zirga-zirga a babbar birnin tarayya, Lagas da kuma jahar Ogun na tsawon kwanaki 14, a matsayin yunkurin hana yaduwar mummunar annobar.
Ya kuma sabonta dokar hana fitan a ranar 13 ga watan Afrilu.

Asali: Twitter
Tuni dai sauran jihohi 36 na kasar suka sanar da wasu matakan hana zirga-zirga duk a kokarin yaki da hana yaduwar cutar coronavirus.
Umurnin gwamnatin ya shafi kotu, kasancewarta daya daga cikin manyan wuraren taron jama’a.
Shugaban alkalan Najeriya, Justis Tanko Muhammad, a ranar 23 ga watan Maris, ya yi umurnin dakatar da duk wani zaman kotu har sai baba-ya-gani, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A wata takarda zuwa ga dukkanin shugabannin kotuna a fadin kasar, Shugaban alkalan kasar, ya ce umurnin ya zama wajibi domin kare alkalai da ma’aikatan kotunan.
Bugu da kari, mukkadashiyar shugabar kotun daukaka kara, Justis Monica Dongban-Mensem, a wata sanarwa ta yi umurnin dakatar da zama a kotun reshen Abuja, Lagas da Ogun. sai dai a kan lamura na gaggawa.
KU KARANTA KUMA: Kwamitin COVID-19 a Katsina ya kashe miliyan N24.6 wajen yiwa masallatai da cocina feshi
Ta ce kotun daukaka karar za ta karfafa amfani da tsarin na’ura wajen zantawa domin rage yawan haduwa kai tsaye a tsakanin lauyoyi, wanda ka iya sanya su kamuwa da COVID-19.
A wani labari na daban, mun ji cewa gwamnatin Seyi Makinde na Oyo, ta roki ‘yan majalisar dokoki su hakura da wani kaso daga cikin kudinsu. Wannan zai taimaka wajen ganin jihar ta samu zama da kafafunta.
Jaridar The Tribune ta bayyana cewa ‘yan majalisar Oyo sun cin ma matsaya da gwamnatin Seyi Makinde game da kason da za a rage daga cikin kudin da su ke karba a kowane wata.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng