Kisan mutane 47 a Katsina: Buhari ya yi alkawarin ramuwar gayya a kan yan bindiga

Kisan mutane 47 a Katsina: Buhari ya yi alkawarin ramuwar gayya a kan yan bindiga

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnati ba za ta lamunci harin da yan bindiga suke kai ma jama’a a jahar Katsina ba, don haka ya yi alkawarin daukan mataki.

Daily Trust ta ruwaito Buhari ya bayyana haka ne biyo bayan mummunan harin da yan bindiga suka kai a kananan hukumomi uku, inda suka kashe mutane 47, tare da jikkata wasu da dama.

KU KARANTA: Ndume ya tubure a kan lallai sai Buhari ya tsige minista Sadiya Umar Farouk

Buhari ta bakin kakaakinsa, Garba Shehu ya ce ba za su bari harin ya wuce haka nan ba har sai sun rama biki da harin ramuwar gayya, wanda yayi daidai da tsarinsa na kare jama’an kasa.

Shugaban ya yi tir da harin tare da bayyana bacin ransa, sa’annan ya umarci hukumomin tsaro su tabbata sun kasance a cikin shiri a kullum don hana yan bindigan sukunin kai hare hare.

Kisan mutane 47 a Katsina: Buhari ya yi alkawarin ramuwar gayya a kan yan bindiga

Kisan mutane 47 a Katsina: Buhari ya yi alkawarin ramuwar gayya a kan yan bindiga
Source: UGC

“Na yi bakin ciki sosai da wannan hari, amma ina kira ga yan Najeriya da kada su karaya saboda gwamnatinmu na iya kokarinta don tabbatar da ta murkushe miyagun dake amfani da damar dokar ta baci da aka sa suna kai ma jama’a hari.” Inji shi.

Daga karshe shugaba Buhari ya jajanta ma iyalan wadanda suka mutu a harin, sa’annan ya nemi jama’a su kasance masu lura da sa ido a unguwanninsu don kai rahoton miyagu.

A ranar Lahadi, 19 ga watan Afrilu ne rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Katsina ta tabbatar da mutuwar mutane 47 a hannun yan bindiga da suka kai munanan hare hare.

Kakaakin rundunar, SP Gambo Isah ya bayyana cewa yan bindigan sun kai harin ne a karamar hukumar Danmusa, karamar hukumar Dutsanma da kuma karamar hukumar Safana.

“A kauyen Kurechin Atai dake Danmusa, sun kashe mutane 14, a Kurechin Dutse da Kurechin Giye na karamar hukumar Dutsan sun kashe mutane 10, a Makauwachi da Daule sun kashe 23.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel