El-Rufa'i, Adamu Adamu, Marwa, da sauran 'yan arewa 6 da ake sa ran za su maye gurbin Abba Kyari

El-Rufa'i, Adamu Adamu, Marwa, da sauran 'yan arewa 6 da ake sa ran za su maye gurbin Abba Kyari

Duk da har yanzu ana juyayi da alhinin mutuwar Abba Kyari, rahotanni sun bayyana cewa tuni dillalan mulki sun fara shige da fice da kulle-kullen fara zawarcin kujerarsa ta shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.

Saurin fara zawarcin kujerar marigayin ba za ta rasa nasaba da muhimmanci da tasirin da ofishinsa keda shi a wajen gudanar da harkokin ofishin shugaban kasa ba.

Jaridar 'The Nation' ta rawaito cewa Mamman Daura, dan uwa sannan amini wurin shugaba Buhari, zai taka muhimmiyar rawa wajen nadin wanda zai maye gurbin marigayi Kyari.

A cewar jaridar, tun asali ma, Mamman Daura ne ya tsayawa marigayi Kyari har ya samu mukamin a karo na farko da na biyu.

A wani rahoto da jaridar ta wallafa ranar Lahadi, ta bayyana cewa akwai 'yan arewa 9 da ake kyautata zaton cewa daga cikinsu Buhari zai zabi madadin marigayi Kyari.

Mutanen 9 sune; tsohon sakataren gwamnatin tarayya sannan tsohon ministan harkokin waje, Babagana Kingibe, ministan ilimi, Adamu Adamu, shugaban hukumar kwastam, Hamid Ali.

Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha, tsohon minista, Ismaila Isa Funtua, gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i, mataimaki na musamman ga shugaban kasa, Ya'u Shehu Darazo.

Ragowar su ne; tsohon gwamnan jihar Legas, Janar Buba Marwa da tsohon babban sakataren fadar shugaban kasa, Jalal Arabi.

El-Rufa'i, Adamu Adamu, Marwa, da sauran 'yan arewa 6 da ake sa ran za su maye gurbin Abba Kyari

Buhari da Abba Kyari
Source: UGC

The Nation ta ce idan har shugaban kasa zai bi ta ra'ayin makusantanshi da ake wa lakabi da 'kabals', za su fi so ya zabi madadin Kyari a tsakanin mutane biyar: Kingibe, Adamu Adamu, Hamid Ali, Darazo da Funtua.

Rahoton jaridar ya bayyana cewa uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta fi son Buhari ya zabi Buba Marwa, wanda suka fito jiha daya, don ya maye gurbin marigayi Kyari.

DUBA WANNAN: Fitattun 'yan Najeriya uku da annobar covid-19 ta hallaka

El-Rufa'i ya shiga cikin jerin mutanen da ake kyautatawa zato ne saboda yawan tuntubarsa da fadar shugaban kasa ke yi kafin gudanar da wasu harkokin mulki.

Akwai wani tsagi na makusanta Buhari da ke kokarin ganin ya maye gurbin marigayi Kyari da SGF Mustapha, saboda biyayyarsa ga shugaba Buhari da kuma kwazonsa na aiki.

Sai dai, a duk cikin mutanen 9, a yanzu haka, babu mai kusanci da shugaba Buhari kamar Malam Adamu Adamu.

Jalal Arabi ya shafe tsawon shekaru 12 ya na aiki a fadar shugaban kasa, kafin daga bisani ya yi ritaya a matsayin babban sakatare a 'yan watannin baya bayan nan.

Ana tunanin cewa shugaba Buhari zai iya zabarsa domin ya maye gurbin marigayi Kyari saboda gogewar da ya ke da ita a harkokin da suka shafi aiki a fadar shugaban kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel