Abba Kyari ne ya yi min babban aboki lokacin da aka daura min aure a Coci a 1984 - Minista
Geoffrey Onyeama, ministan harkokin waje, ya ce marigayi Abba Kyari ne ya yi masa babban aboki lokacin da aka daura masa aure a Cocin katolika, shekaru ma su yawa da su ka gabata.
Ango ya na zabar babban aboki ne daga cikin aminansa, wanda kuma zai zama shaidarka na yin aure a tsarin addinin Kirista.
A sakon ta'aziyya da ministan ya fitar, Onyeama ya ce marigayi Kyari ne ya zama uba na musamman ga dansa yayin da aka yi ma sa a baftisma.
A cikin sakon da ya fitar ranar Lahadi, Oyeama ya bayyana cewa ya fara haduwa da marigayi Kyari a shekarar 1977 a jami'ar Warwick da ke kasar Ingila.
Onyeama ya bayyana cewa ba zai taba manta yadda shugabannin Cocinsa su ke nuna mamakinsu a fili ba duk lokacin da su ka marigayi Kyari a matsayin babban amininsa duk da kasancewarsa Musulmi.
DUBA WANNAN: 'A gafarce mu' - NCDC ta gyara aringizon da ta yi a alkaluman masu dauke da cutar covi-19 a Najeriya
Ministan ya ce shi da marigayi Kyari sun kasance aminai da koda yaushe ke tuntubar juna a tsawon shekaru 43 da su ka yi da sanin juna.
A cewar ministan, marigayi Kyari ya sha ziyartarsa lokacin da ya ke aiki a Geneva, kuma duk lokacin da ya zo Najeriya sai sun hadu, saboda zumuncin da ke tsakaninsu.
"Marigayi Kyari dan kishin kasa ne mai akidar cigaba da ba ya nuna wariya saboda banbancin kabila ko addini," a cewar Onyeama.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng