Ganganci: Magidanci ya datse hannun matarsa saboda ta fita unguwa ba izininsa

Ganganci: Magidanci ya datse hannun matarsa saboda ta fita unguwa ba izininsa

Rundunar 'yan sanda a jihar Yobe ta sanar da kama wani mutum mai suna Baari Bacha wanda ya datse hannun matarsa, Halima Bulama.

A cewar rundunar 'yan sanda, Bacha ya datse hannun Halima da gangan saboda ta ki bin umarninsa a kan hanata fita zuwa wurin wani biki ba tare da izininsa ba.

"Fitar da ta yi ne babu izininsa ya fusata shi har ta kai ga ya dauko wata adda ya datse mata hannu yayin da su ke tsaka da cacar baki bayan ta dawo gida," a cewar wata majiya.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Yobe, Dungus Abdulkarim, ya bukaci jama'a su kwantar da hankalinsu.

Ya kara da cewa yanzu haka Halima ta na samun kulawa a wani asibiti tare da bayyana cewa za a gurfanar da Bacha a gaban kotu da zarar an kammala bicike.

Ganganci: Magidanci ya datse hannun matarsa saboda ta fita unguwa ba izininsa
Ganganci: Magidanci ya datse hannun matarsa saboda ta fita unguwa ba izininsa
Asali: Twitter

A wani labarin daga jihar Kaduna, wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da mata ma su jego guda uku a kauyen Karaukarau da ke karamar hukumar Giwa.

DUBA WANNAN: Jami'an tsaro sun kashe mutane 18 yayin tabbatar da dokar zaman gida a Najeriya - NHRC

Wani mazaunin kauyen mai suna Malam Sani Bakali ya shaidawa wakilin jaridar 'The Nation' cewa 'yan bindigar, dauke da muggan makamai, sun fara yunkurin tafiya da mata 13 daga kauyen.

Ya kara da cewa mazauna kauyen sun cire tsoro, sun tunkari 'yan bindigar tare da hanasu tafiya da dukkan matan 13.

Bakali ya bayyana cewa, 'yan bindigar da su ka dira a kauyen ranar Talata, sun yi awon gaba da ma su jegon yayin da ake wani bikin aure.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel