'A gafarce mu' - NCDC ta gyara aringizon da ta yi a alkaluman masu dauke da cutar covi-19 a Najeriya

'A gafarce mu' - NCDC ta gyara aringizon da ta yi a alkaluman masu dauke da cutar covi-19 a Najeriya

Hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) ta bayyana cewa ta yi kuskure a alkaluman ma su dauke da kwayar cutar covid-19 da ta yada ranar Asabar da daddare.

A daren ranar Asabar ne hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) ta sanar da samun karin sabbin mutane 49 da suka kamu da kwayar cutar covid-19 a fadin Najeriya.

A cikin sanarwar da ta fitar a shafinta na tuwita, NCDC ta ce an samu karin sabbin mutane 23 da suka kamu da kwayar cutar Legas, 12 a Abuja da karin wasu 10 daga jihar Kano.

Sauran jihohin da aka tabbatar da samun ma su dauke da kwayar cutar sun hada da jihar Ogun; mutum biyu, sai jihar Oyo da jihar Ekiti ma su mutum daya kowannensu.

A cikin wata sanarwa da NCDC ta fitar da safiyar ranar Lahadi, ta bayyana cewa ta yi kuskure wajen sanar da cewa an samu mutum daya da ya kamu da wayar cutar a Ekiti.

"Mun yi kuskuren sanar da cewa an samu mutum daya mai dauke da kwayar cutar covid-19 a jihar Ekiti. An samu kuskuren ne wajen tattara alkaluman ma su dauke da kwayar cutar.

"A saboda haka, jimillar ma su dauke da kwayar cutar ya zuwa ranar Asabar, 18 ga watan Afrilu, ya zama 541, an sallami mutane 166 da su ka warke, mutane 19 ne kwayar cutar covid-19 ta kashe.

"Mutane uku ne aka tabbatar da cewa su na dauke da kwayar cutar a jihar Ekiti, ba mutum hudu ba," a cewar NCDC.

DUBA WANNAN: Fitattun 'yan Najeriya uku da annobar cutar covid-19 ta hallaka

A cikin gyran da ta yi a kan alkaluman da ta fitar a daren ranar Asabar, NCDC ta fitar da jerin jihohi da adadin ma su cutar a kowacce jiha kamar haka;

Lagos- 306

FCT- 81

Kano- 37

Osun- 20

Oyo- 16

Edo- 15

Ogun- 12

Kwara- 9

Katsina- 9

Bauchi- 6

Kaduna- 6

Akwa Ibom- 6

Delta- 4

Ekiti- 3

Ondo- 3

Enugu- 2

Rivers-2

Niger- 2

Benue- 1

Anambra- 1

NCDC ta nemi afuwar gwamnatin jihar Ekiti a kan kuskuren da aka samu tare da bayyana aniyarta na iganta aikinta da sanar da jama'a gaskiyar al'amura a kan annobar covid-19.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel