Buhari: Abba Kyari Aminina ne shekara 42, kuma katangar fadar Shugaban kasa

Buhari: Abba Kyari Aminina ne shekara 42, kuma katangar fadar Shugaban kasa

Kawo yanzu dai labari ya gama game Duniya cewa mummunar cutar nan ta Coronavirus ta kashe shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar Najeriya watau Abba Kyari.

A jiya Asabar ne shugaba Muhammadu Buhari ya rubuta wata wasika ga Marigayin wanda ya kasance Amininsa na tsawon shekaru. Ga abin da mu ka tsukuro daga wasikar:

1. Aminin Shugaba Buhari na shekaru 42

Shekaru 42 da su ka wuce zuwa yanzu, Abba Kyari ya kasance abokin Muhammadu Buhari na kut-da-kut. Alakar wadannan bayin Allah ta kasance cike da rikon amana da yarda da juna.

2. Zakakurin Mai basira

A lokacin da Abba Kyari ya ke ‘dan makaranta, ya na da hazaka, wannan ya sa ya samu damar karatu a kasashen waje. Kyari ya yi Digiri a Jami’ar Warwick da kuma Harvard ta Amurka.

KU KARANTA: Jibrin ya soki yadda aka kyale jama'a su na jifan Kyari a lokacin rayuwarsa

3. Bai kamu da giyan mulki ba

Ko da Abba Kyari ya samu matsayi mai tsoka a Najeriya, bai bari giya da gigin mulki sun dauke shi ba. A wasikar ta’aziyyar shugaba Buhari, ya bayyana Kyari a matsayin mutum mai gaskiya.

4. Mutum mai zurfin ciki

Marigayi Abba Kyari mutum ne mai rike sirri wanda kuma ba ya neman kanzagin jama’a. Har Kyari ya rasu, bai kasance ya na yin abu domin abin da mutane za su fada ba inji Maigidansa.

5. Katangar shugaban kasa Buhari

Marigayi Kyari ya zama wani shamakin karfe tsakanin jama’a da shugaba Muhammadu Buhari. Babu wanda ya isa ya ratsa shugaban kasa sai ta hannunsa, kuma ya yi wa kowa adalci.

6. Abba Kyari ya na da kishin-kasa

Malam Abba Kyari ya kasance mutum ne mai nuna kishin kasa a maganganunsa da ayyukansa. Kyari bai nuna banbanci wajen aiki saboda sabanin kabila, addini ko martaba da dangi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel