Wasu Masoya da Makiya da su ka fito su na yabon Abba Kyari bayan ya rasu

Wasu Masoya da Makiya da su ka fito su na yabon Abba Kyari bayan ya rasu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatinsa da ‘yan Najeriya su na makokin rasuwar Malam Kyari wanda ya kasance kafin rasuwarsa babban hadimin shugaban kasa.

Mutane sun fito su na fadin abin da su ka sani a kan Marigayi Abba Kyari bayan cikawarsa. Daga ciki har da wadanda su ka yi fice a adawa da sukar gwamnatin Muhammadu Buhari.

Feyi Fawehimi wanda ya kan soki tsare-tsaren gwamnatin APC ya na cikin wadanda mutuwar wannan Ta’aliki ya yi masu ciwo. Fawehimi ya ce Abba Kyari mutumin kwarai ne.

A cewar wani hadimin shugaban kasa mai suna Bashir Ahmaad, Abba Kyari ya na cikin wadanda aka yi wa mummunar shaida, amma duk wanda ya san shi, ya san mutumin kirki ne.

Shi ma Omasoro Ali Ovie wanda ya saba fadin alherin gwamnatin shugaban kasa Buhari, hakan ya fada, ya ce: "(Kyari) Shi ne mutumin da aka fi yi wa kuskuren fahimta a Najeriya."

Tsohon ministan Najeriya Femi Fani-Kayode wanda ya na cikin manyan ‘yan adawan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kira fadar shugaban kasa har ya yi masu ta’aziyya.

KU KARANTA: Musulmai na kyautata zaton Abba Kyari ya yi shahada Inji Pantami

“Na rasa Abokin shekaru 40. Mun kasance tare a jami’ar Cambridge. Mun yi aikin shari’a tare a karkashin mahaifina. Mun kasance tare da shi na duk tsawon shekarun nan.

Fani-Kayode ya ce duk da banbancinsa a fuskar siyasa da Fani-Kayode, babu shakka Marigayin abokin kwarai ne kuma wanda ya san halacci. Kayode ya yi masa addu’a a karshe.

A game da Kyari, Sanata Shehu Sani cewa ya yi: “Shugaban kasa ya rasa amintaccen aboki. mutumin da ya shanye gular maigidansa, ya na murmushi ba tare da ya ce uffan ba.

Tsohon Sanatan ya ce Marigayi Abba Kyari ya bar Duniya ba tare da ya sanar da jama’a na sa bangaren labarin ba domin a san gaskiyar duk abin da ake fada a game da shi ba.

Reno Omokri ya yi tir da masu sukar Marigayin a wannnan lokaci. Omokri ya bayyana Kyari da amana, ya ce: “Duk da banbancinmu da shi, ya kasance mai kaunar Najeriya.”

Tsohon ‘dan majalisar tarayya Abdulmumin Jibrin Allah-wadai ya yi da masu yabon Marigayin a yanzu, ya zarge su da yin gum a lokacin da ake sukan Kyari sa'ilin ya na da rai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel