Abba Kyari: Dangote, Atiku, Jonathan sun yi wa Buhari da Najeriya ta’aziyya

Abba Kyari: Dangote, Atiku, Jonathan sun yi wa Buhari da Najeriya ta’aziyya

A ranar Asabar ne aka yi jana’izar Marigayi Abba Kyari a wata babbar makabartar Musulmai da ke garin Abuja. Abba Kyari ya rasu ne bayan ya yi jinyar cutar Coronavirus a Najeriya.

Mutane da-dama sun fito su na jimami da ta’aziyyar wannan rashi da Najeriya ta yi na babban Hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda kowa ya san da zaman shi a kasar.

Tsohon shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan ya na cikin wadanda su ka aikawa shugaba Muhammadu Buhari da kuma Iyalin Marigayin ta’aziyya na wannan rashi da su ka yi.

“Ina yi wa mai girma Muhammadu Buhari, da Iyalin Abba Kyari da duk masu makokin Mallam Abba Kyari wanda kafin rasuwarsa shi ne shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar Najeriya ta’aziyya. Ina rokon Allah ya ba shi Aljannar Firdausi kuma ya karawa Iyalai da Abokansa hakuri a wannan lokaci na makoki” Inji Goodluck Jonathan a shafinsa na Tuwita a jiya Asabar.

KU KARANTA: Abubuwan da ke zagaye da ajalin babban Hadimin Shugaban Najeriya

Shi kuwa tsohon mataimakin shugaban kasa kuma Jagoran adawa a Najeriya, Atiku Abubakar, sallati ya fara kwatsamawa a sakon ta’aziyyar da ya fitar a jiya ranar Asabar da safe.

Alhaji Atiku ya ce: “Inna lillahi wa inna ilayhi raji'un. Na yi bakin ciki da mutuwar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari. Allah ya ba Iyalinsa karfin ikon hakuri.”

Bayan addu’a ga Iyalin Mamacin na jure wannan rashi, Wazirin na Adamawa ya kara da cewa: “Allah ya yafe masa zunubansa, ya kuma datar da shi da Aljannar Firdaus. Ameen.”

Aliko Dangote cewa ya yi: “Labarin mutuwar ‘danuwa kuma mai kishin kasa, hadimi Abba Kyari ya yi mani nauyin ji. Najeriya ta yi rashin zakakuri, mai basira kuma wanda ya san aiki”

A jawabin da ya yi a Tuwita, Aliko Dangote ya yi wa Iyalin marigayin da kuma shugaban kasa da mutanen Najeriya ta’aziyya. Attajirin ya kuma yi wa Marigayin addu’ar dace da Aljanna.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel