Ana sa ran cewa Marigayi Malam Abba Kyari ya yi mutuwar shahada

Ana sa ran cewa Marigayi Malam Abba Kyari ya yi mutuwar shahada

A ranar Juma’ar nan ne Najeriya ta girgiza da mutuwar babban Hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari watau Abba Kyari a sakamakon fama da cutar COVID-19.

Tuni aka yi jana’izar Malam Abba Kyari wanda ya kasance shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa na kusan tsawon shekaru biyar. Kyari ya bar Duniya ya na da shekara 67.

Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami wanda ya sallaci gawar Abba Kyari ya bayyana cewa ana kyautatawa Mamacin zaton ya yi mutuwar shahada ganin irin halin da ya cika.

Isa Ali Ibrahim Pantami ya nuna cewa Marigayi Abba Kyari ya dace da manyan rabo kamar yadda addinin Musulunci ya nuna, daga ciki shi ne ya rasu a rana mai girma ta Juma’a.

Malamin addinin ya shaidawa tsirarrun mutanen da su ka halarci janazar wannan Bawan Allah cewa ana kyautatawa duk wani mai imani da ya mutu a ranar Juma’a zaton dace.

KU KARANTA: Za a tirke wadanda su ka halarci sallar janazar Marigayi Abba Kyari

Ana sa ran cewa Marigayi Malam Abba Kyari ya yi mutuwar shahada
Sheikh Pantami ya na kyautata zaton Marigayi Kyari ya dace da shahada
Asali: Twitter

A wani hadisin Manzon Allah SAW da Shehin Malamin ya ambata, ya ce alamun karshen Mutum ya yi kyau, shi ne ya mutu a wannan rana. Kyari ya kuwa cika ne a ranar Juma’a.

Bayan haka, Sheikh Isa Ali Pantami ya ambaci wani dacen da amintaccen Hadimin na shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi, wannan kuwa shi ne mutuwa a lokacin annoba.

Shi ma wani Hadisi ya tabbata daga bakin Manzon Allah SAW cewa duk Mutumin da annoba ta ga karshensa ya na mai cikakken imani, ya mutu Mutumin Aljanna inji Malamin.

Marigayi Kyari ya shafe tsawon makonni ya na jinyar cutar Coronavirus a wani asibitin kwararru da ke Legas. A karshe dai wannan mugun ciwo ne ya yi karshen wannan Dattijo.

A karshen bayanin Sheikh Pantami ya yi kira ga jama’a su bi doka, su kauracewa zuwa gaisuwar makoki a wannan hali. Malamin wanda yanzu Minista ne ya ce hakan al’adace.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel