Manyan mutane uku da annobar covid-19 ta hallaka

Manyan mutane uku da annobar covid-19 ta hallaka

An fara samun bullar cutar covid-19 ne a garin Wuhan da ke kasar China a cikin watan Disamba na shekarar 2019, kuma tun bayan wannan lokacin annobar ke cigaba da mamaye sassan duniya.

Kiyasi ya nuna cewa an tabbatar da samun kwayar cutar a jikin mutane fiye da miliyan biyu a fadin duniya tare da kashe mutanen da yawansu ya haura dubu dari.

An fara samun bullar annobar a Najeriya a cikin watan Fabrairu ta hannun wani baturen kasar Italiya da ya sauka a jihar Legas.

Ya zuwa daren ranar Asabar, 18 ga watan Afrilu, annobar cutar covid-19 ta hallaka mutane 19 a Najeriya.

An sallami jimillar mutane 166 daga cibiyoyin killacewa da ke fadin kasar nan bayan an tabbatar da warkewarsu.

Daga cikin mutanen da annobar ta hallaka, akwai wasu fitattun 'yan Najeriya uku

1. Suleiman Achimugu

Suleiman Achimugu, tsohon shugaban bangaren PPMC a NNPC, shine mutum na farko da aka fara sanar da cewa annobar cutar covid-19 ta kashe a Najeriya.

Tsohon shugaban na PPMC, mai shekaru 67 a duniya, ya mutu ne ranar 22 ga watan Maris bayan dawowarsa daga kasar Ingila.

2. Victor Ikwuemesi

Wani fitaccen dan Najeriya da annobar cutar covid-19 ta hallaka shine Victor Ikwuemesi, tsohon shugaban tsohon kamfanin jiragen sama na 'Sosoliso'

Ya mutu ne a Ingila bayan an tabbatar da cewa ya kamu da kwayar cutar a kasar.

3. Abba Kyari

Farfesa Akin Abayomi, kwamishinan lafiya a jihar Legas, ya ce marigayi Abba Kyari, tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, ya mutu ne a wani asibitin kwararru da ake duba ma su ciwon zuciya.

A ranar Juma'a ne fadar shugaban kasa ta sanar da mutuwar Kyari, an binne shi ranar Asabar bisa tsarin addinin Musulunci.

DUBA WANNAN: Manyan annoba 6 da aka taba yi a duniya da adadin mutanen da kowacce ta hallaka

A cikin wani jawabi da ya fitar ranar Asabar a shafinsa na Tuwita domin amsa tambayoyi a kan mutuwar Kyari, Farfesa Abayomi ya ce asibitin da aka kwantar da Kyari ya samu sahalewar hukuma domin duba ma su cutar covid-19.

A ranar Juma'a ne ministan lafiya, Dakta Osagie Ehanire, ya bayyana cewa ya zuwa yanzu babu wani asibiti mai zaman kansa da aka bawa lasisi ko izinin duba ma su fama da cutar covid-19.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel