Cikakken bayanin shugaba Buhari game da rasuwar Abba Kyari

Cikakken bayanin shugaba Buhari game da rasuwar Abba Kyari

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi jawabi na bankwana ga tsoshon shugaban maaiktan fadarsa kuma amininsa na tsawon shekaru, Mallam Abba Kyari da cutar coronavirus ta yi ajalinsa bayan ya yi jinya na makonni.

Ga abinda sakon na shugaba Buhari ya kunsa

Zuwa ga abokina, Mallam Abba Kyari,

Mallam Abba Kyari, wanda ya rasu a ranar 17 ga watan Afirilun 2020 ya rasu ne yana da shekaru 67 sakamakon cutar coronavirus da ya kamu da ita.

Na rasa abokin shekaru 42 kuma shugaban ma'aikatan fada ta. Bai taba nuna gazawarsa ba wajen tabbatar da ci gaba.

Yana cikin shekarunsa na 20 ne a lokacin da muka fara haduwa. Dalibi ne mai kwazo wanda babu dadewa ya samu gurbin karatu a kasar waje.

Ya yi karatu a jami'ar Warwick kafin daga bisani ya koma Cambridge. Amma babu shakka, Abba ya dawo da kwazonsa da hazakarsa don amfanin kasarsa.

A yayin da yake daga cikin masu ruwa da tsaki a gwamnatin nan, kullum maganarsa shine yadda za a inganta ababen more rayuwa da kuma tsaro a kasar nan.

Don yasan cewa in har babu su, babu wani ci gaba da 'yan Najeriya za su samu wanda suka cancanta.

A fannin siyasa, Abba bai taba neman kujerar siyasa da kansa ba. A maimakon haka, ya saka kansa a cikin jama'ar da ke gani cewa tushen rashawa yana nan ne a ofisoshin siyasa.

Cikakken bayanin shugaba Buhari game da rasuwar Abba Kyari

Cikakken bayanin shugaba Buhari game da rasuwar Abba Kyari
Source: UGC

DUBA WANNAN: Abubuwa 4 masu rikitarwa game da mutuwar Abba Kyari

Koda yake a shugaban ma'aikatan fadata tun daga 2015, yana aiki ne cikin kwanciyar hankali da kuma rashin bukatar yin suna.

Akwai wadanda ke cewa yana cikin mutane masu sirri saboda mutane basu sanin abinda yake ciki.

Amma kuma ba hakan bane, baya bukatar jinjina da yabawar jama'a ne. A wurinsa, babu wani abin bukata na yin suna a wurin mutane.

Yana yin komai ne don samun lada daga mahaliccinsa tare da inganta shugabanci na gari a kasar nan.

Yana aiki babu tsayawa na kwanaki bakwai na ranakun sati, babu ranakun karshen mako. Yana tabbatar da cewa kowanne gwamna ko minista duk daya suke.

Kiri-kiri yake bayyana cewa kowannen dan Najeriya ba tare da duban addini ko kabila ba duk daya suke.

Mallam Abba Kyari mutum ne mai matukar nagarta. Yana daga cikin masu inganta kasar nan. Ina fatan abokina na masauki nagari.

Ga matarsa da iyalansa da ya bari, ina musu ta'aziyya tare da taya alhinin rashinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel