Abba Kyari: Atiku ya yi tsokaci a kan mutuwar shugaban ma’aikatan shugaban kasa

Abba Kyari: Atiku ya yi tsokaci a kan mutuwar shugaban ma’aikatan shugaban kasa

- Atiku Abubakar ya yi tsokaci a kan mutuwar Abba Kyari, shugaban ma’aikatan shugaban kasa Buhari

- Tsohon mataimakin shugaban kasar, ya ce ya kadu da mutuwar Kyari

- Atiku wanda ya kasance dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2019, ya yi addu’an Allah ya yafe ma Kyari zunubansa sannan ya bashi Aljannah

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya mika ta’aziyyarsa a kan mutuwar Abba Kyari, shugaban ma’aikatan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Fadar shugaban kasa ta sanar da mutuwar Kyari a safiyar ranar Asabar, 18 ga watan Afrilu.

Marigayin ya kamu da cutar COVID-19 sannan kuma yana ta samun kulawar likitoci a wani wuri da ba a bayyana ba.

Abba Kyari: Atiku ya yi martani a kan mutuwar shugaban ma’aikatan shugaban kasa
Abba Kyari: Atiku ya yi martani a kan mutuwar shugaban ma’aikatan shugaban kasa
Asali: UGC

Sai dai kuma, ya rasu a ranar Juma’a, 17 ga watan Afrilu, kamar yadda sanarwa daga kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya nuna.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Fadar shugaban kasa ta bayyana shirye-shiryen jana'izar Abba Kyari

A tsokacinsa, Atiku yace:

"Inna lillahi wa inna ilayhi raji'un. Na yi bakin ciki da mutuwar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari. Allah SWT ya karawa a iyalansa hakuri, Allah ya ji kansa ya yafe masa kura-kuransa, ya saka masa da Aljannah Firdaus. Ameen.”

Labarin yadda ya kamu da cutar ta Coronavirus dai ya fito ne a watan Maris, inda bayan kamuwarshi da cutar, shi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari aka yi masa gwaji ba a samu cutar a jikinshi ba.

Shugaba Buhari, Yemi Osinbajo, gwamnoni da ministoci da dama sun hadu da shi kafin a gabatar da gwajin cutar a jikinshi.

Kyari wanda ya dawo Najeriya daga wata tafiya da yayi zuwa kasar Jamus, a ranar 14 ga watan Maris, ya gana da manyan mutane na Najeriya da dama.

Abba Kyari daga baya ya fito ya bayyana cewa za a kai shi birnin Legas daga Abuja domin ya cigaba da karbar magani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel