Abba Kyari ya fada mani cewa yana nan lafiya – Festus Keyamo
- Karamin ministan kwadago da daukar ma’aikata, Festus Keyamo, ya yi martani ga mutuwar Abba Kyari, shugaban ma’aikatar Shugaban kasa
- Keyamo ya bayyana a shafin Twitter cewa ya tattauna da Abba Kyari a ranar Talata, 24 ga watan Maris, kafin mutuwarsa
- Ministan ya ce marigayin ya fada masa cewa yana nan lafiya sannan cewa shi (Kyari) zai karbi duk wani magani da za a yi masa
Karamin ministan kwadago da diban ma’aikata, Festus Keyamo, ya kasance dan Najeriya na farko da ya yi martani ga mutuwar Abba Kyari, shugaban ma’aikatan shugaban kasa.
Keyamo ya bayyana a shafin Twitter cewa ya tattauna da Mallam Abba Kyari a ranar Talata, 24 ga watan Maris, kafin mutuwar dan siyasar.

Asali: UGC
A cewar ministan, a lokacin tattaunawarsu, marigayi shugaban ma’aikatan tarayyar ya fada masa cewa yana nan lafiya kuma cewa shi (Kyari) zai amshi duk wani magani da za a yi masa cikin aminci.
Keyamo wanda ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan Kyari kan mutuwar shugaban ma’aikatan shugaban kasar ya ce, a koda yaushe Allah ya san abunda ya fi dacewa.
“A lokacin da na yi hira dashi a ranar Talata, 24 ga watan Maris, 2020, ya bani tabbacin cewa yana cikin koshin lafiya sannan cewa zai amshi duk wani magani da za a yi masa cikin aminci” in ji ministan.
KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Shugaban ma'aikatan Najeriya Abba Kyari ya riga mu gidan gaskiya
“Amma a koda yaushe Allah ya san abunda ya fi dacewa. Ina mika ta’aziyyata ga iyalan Kyari da gwamnatin Najeriya. Allah ya ji kan Mallam Abba Kyari."
A halin da ake ciki, mun ji cewa za a birne Marigayi Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari a garin Abuja a yau Asabar, jaridar Premium Times ta gano.
Kyari dan asalin jihar Borno ne. An sanar da rasuwarsa ne a jiya Juma’a bayan jinyar da ya kwanta sakamakon kamuwa da yayi da coronavirus.
An gano yana dauke da cutar ne a ranar 23 ga watan Maris kuma an kaishi jihar Legas don jinya.
Bayan rasuwarsa a daren Juma’a, fadar shugaban kasa ta fara shirin birne shi kamar yadda addinin Islama ya tanadar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng