Yanzu-yanzu: An sake samun mutum 2 dauke da Covid-19 a Katsina

Yanzu-yanzu: An sake samun mutum 2 dauke da Covid-19 a Katsina

An sake samun mutum biyu dauke da cutar coronavirus a jihar Katsina. Wannan ne ya kai jimillar masu cutar zuwa 9 a jihar kamar yadda hukumar hana yaduwar cututtuka (NCDC) ta bayyana.

Shugaban kwamitin yaki da coronavirus na jihar Katsina, Mannir Yakubu, ya sanar da hakan a yau Juma'a da yammaci yayin zantawa da manema labarai a gidan gwamnatin jihar Katsina.

Jaridar The Nation ta bayyana cewa, NCDC ta wallafa a shafinta na twitter cewa an samu mutum bakwai dauke da cutar a jihar a ranar Alhamis.

Amma kuma a yau Juma'a, an sake samun wasu mutum biyu dauke da cutar tare da tarin mutanen da suka yi mu'amala dasu. Tuni dai an ganosu tare da daukar samfur don gwaji.

Mannir, wanda shine mataimakin gwamnan jihar Katsina, ya ce kwamitin ya samu karin mutum hudu masu dauke da cutar a ranar 16 ga watan Afirilun 2020.

Yanzu-yanzu: An sake samun mutum 2 dauke da Covid-19 a Katsina

Yanzu-yanzu: An sake samun mutum 2 dauke da Covid-19 a Katsina
Source: UGC

DUBA WANNAN: COVID-19: Masari ya dakatar da sallar Tarawihi da Juma'a, ya kuma sake rufe wata karamar hukuma

Ya ce, "Da farko jihar tana da mutum bakwai da ke dauke da cutar, yanzu an samu karin mutum biyu wanda hakan ya kai jimillar zuwa mutum tara.

"Daga cikin mutum hudu na farko da aka samu, duk daga karamar hukumar Daura suke".

Ya kara da cewa sauran masu dauke da cutar daga karamar hukumar Dutsinma ne da suka kai ziyara jihar Legas.

Ya kara da bayyana cewa, kwamitin ya samu Naira miliyan 200 ta wurin masu bada gudumawa don yaki da cutar a jihar. Akwai wata Naira miliyan 33.5 da aka yi alkawarin bayar wa gudumawa.

Mannir ya ce ana tunanin kafa cibiyoyin killacewa bakwai a jihar. Daura, Baure, Funtua, Malumfashi, Dutsinma, Kankia da Jibia ne ake duba a matsayin yankunan da za a kara kafa cibiyoyin.

Ya ce kwamitin ya horar da ma'aikatan lafiya 66 don kafa cibiyoyin killacewar wanda ya ci Naira miliyan 3.7.

An fara samun cutar coronavirus a jihar Katsina ne tun bayan mutuwar wani likita a karamar hukumar Daura.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel