Jahar Kano ta mika wani mutum da ya kamu da cutar Coronavirus ga gwamnatin Jigawa
Gwamnatin jahar Jigawa ta sanar da samun mutum na farko dake dauke da annobar cutar Coronavirus, dan asalin jahar Jigawa.
Wani jami’i ya bayyana cewa an turo mutumin jahar Jigawa ne daga jahar Kano, inda a can ne aka gudanar da gwaji a kansa har aka tabbatar da kamuwarsa da cutar.
KU KARANTA: Da dumi dumi: Shugaban kwamitin yaki da Coronavirus a Kano ya kamu da cutar
Premium Times ta ruwaito mutumin matashi ne mai shekaru 26 dan asalin karamar hukumar Kaugamawa, da ya dawo daga jahar Legas.
A kan iyakar jahar Jigawa da Kano jami’in kiwon lafiya na jahar Kano suka kama shi, daga bisani aka gudanar da gwajin cutar Corona akansa, sakamakon gwaji ya tabbatar da hakan.
Kwamishinan ma’aikatar kiwon lafiya ta jahar Jigawa, Abba Zakari ya bayyana cewa a yanzu haka mutumin yana cibiyar killace masu cutar, kuma yana samun lafiya.

Asali: Facebook
“Su biyu ne aka samu yan asalin jahar Jigawa da suka dawo daga jahar Legas, an yi musu gwaji, daya ya kamu, daya kuma bai kamu ba, a yanzu haka suna cibiyar killace masu cutar.” Inji shi.
Kwamishinan ya bayyana wasu matakai da suka dauka a jahar Jigawa don kare yaduwar cutar, inda yace an umarci duk masu zuwa Masallatan Juma’a su yi amfani da abin rufe fuskokinsu.
Haka zalika an nemi Masallatan su tsaya nesa nesa da juna, kimanin mita bibbiyu a tsakani domin kare kansu daga kamuwa da cutar, ko yaduwarta a cikin jama’a.
Gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru da kansa ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, jim kadan bayan wata ganawa da yayi da sarakunan jahar da sauran masu ruwa da tsaki inda yace:
“Duba da irin abin da yake faruwa a jahar Kano, muna kira ga sarakuna da majalisar malamai su duba tsare tsaren da muka tanadar domin ganin yadda zamu kare jama’anmu ba tare da tsawwala musu ba.
“Shawarar da aka yanke shi ne za mu cigaba da gudanar da sallar Juma’a, amma fa da amincewar za’a bada tazarar mita 2 a dukkanin Masallatai, kuma kowa zai rufe fuskarsa da kyalle ko da ihrami.” Inji shi.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng