Kano: Mummunan hatsarin mota ya halaka mutum 14, 8 sun jikkata

Kano: Mummunan hatsarin mota ya halaka mutum 14, 8 sun jikkata

- Mutum 14 ne suka rasa rayukansu sakamakon mummunan hatsarin mota da ya auku a kan titin Wudil zuwa Kano

- Mota kirar Hiace ta dauko mutane 22 amma sai taya ta fashe mata a kan titin, kamar yadda shugaban FRSC na yankin ya tabbatar

- A cikin mutum 14 da suka rasa rayukansu akwai biyu maza, bakwai mata sai biyar kananan yara

Mutum 14 ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da mutum 8 suka samu raunika daban-daban sakamakon hatsarin da aka yi kusa da kauyen Makole da ke kan titin Wudil zuwa Kano a jihar Kano.

Kwamandan yankin na hukumar kiyaye hadurra na jihar Kano, Zubairu Mato ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya aika wa jaridar Daily Trust a ranar Juma'a.

Zubairu ya ce hatsarin ya faru wajen karfe 10:40 na daren a ranar Alhamis.

Ya ce wata motar haya kirar Hiace mai dauke da fasinjoji 22 ce tayarta ta fashe. Hakan ya yi sanadin mutuwar mutum 14 daga ciki.

Kwamandan FRSC din na jihar ya danganta hatsarin da daukar fasinjoji fiye da ka'ida. Ya ce mutum 22 sun yi matukar yawa a cikin motar.

Kano: Mummunan hatsarin mota ya halaka mutum 14, 8 sun jigata
Kano: Mummunan hatsarin mota ya halaka mutum 14, 8 sun jigata
Asali: Twitter

KU KARANTA: COVID-19: Masari ya dakatar da sallar Tarawihi da Juma'a, ya kuma sake rufe wata karamar hukuma

Ya kara da cewa maza biyu, mata bakwai da yara biyar ne suka rasa rayukansu.

"Hatsarin ya faru ne wajen karfe 10:40 na daren Alhamis. Muna samun labari muka gaggauta tura jami'anmu da ababen hawa don ceto wadanda abin ya ritsa dasu.

"An mika su babban asibitin Wudil inda aka adana gawawwaki 14 a ma'adanar gawawwaki ta asibitin. Mutum 8 din da suka samu raunika na karbar kulawar likitoci," yace.

Ya kara da cewa 'yan sandan yankin Gano sun taimaka wajen ceto rayukan wadanda suka yi hatsarin.

A wani labari na daban, Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari ya sanar da dakatar da yin sallar tarawihi da sallar Juma'a a cikin jam'i kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Gwamnan ya kuma datse shige da fice a karamar hukumar Dutsinma na jihar inda aka samu bullar coronavirus a jihar a ranar Laraba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel