Gobara ta tashi a dakin ajiye magunguna a Kebbi

Gobara ta tashi a dakin ajiye magunguna a Kebbi

- Gobara ta tashi a babban dakin ajiye magunguna na cibiyar kula da zazzabin cizon sauro, da ke Birnin-Kebbi

- Lamarin ya afku ne a daren ranar Alhamis, 16 ga watan Afrilu

- An yi nasarar tsiratar da tarin magunguna daga gobarar sai dai duk da haka wasu sun kone

Babban dakin ajiye magunguna na cibiyar kula da zazzabin cizon sauro, da ke Birnin-Kebbi ya kama da wuta, a daren ranar Alhamis, 16 ga watan Afrilu.

An yi nasarar tsiratar da tarin magunguna daga gobarar.

Gobarar ta kwashe tsawon sa’o’i hudu kafin wasu tawaga da suka hada da masu tausayi, gwamnan jahar Abubakar Atiku Bagudu.

Sauran sune; shugaban ma’aikatan gwamnatin jahar Alhaji Suleiman Muhammad Argungu da sakataren gwamnatin, Alhaji Babale Umar Yauri suka taimaka wajen kashe wutar.

Yanzun nan: Gobara ta tashi a dakin ajiye magunguna a Kebbi
Yanzun nan: Gobara ta tashi a dakin ajiye magunguna a Kebbi
Asali: UGC

Har ila yau cikin wadanda suka taimaka harda kwamishinan yan sanda, Daraktan ma’aikatar tsaro na jahar, kwamandan hukumar sibul defence na jahar, da jami’an hukumar kasha gobara.

Bagudu ya yi godiya ga dukkanin bayin Allah da suka bayar da gudunmawa wajen kashe gobarar.

Ya bayyana cewa gobarar bata yi wa kayayyakin dakin ajiyar barna ba sosai, domin an yi nasarar tsiratar da mafi akasarin kayan.

Sai dai, an yi asarar yan wasu kayayyaki, magunguna, amma ba a san adadinsu ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Ana gobara a Hedkwatar INEC dake Abuja

A wani labarin kuma, mun ji cewa 'Yan gudun hijira 14 ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da 15 daga ciki suka samu raunika daban-daban.

Hakan ya faru ne sakamakon barkewar gobara a sansanin 'yan gudun hijarar da ke karamar hukumar Ngala ta jihar Borno.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana, gobarar ta fara ne da karfe 2:15 na yammacin ranar Alhamis a sansanin.

A lokacin da majiyar ke sanarwa, ana ci gaba da kwashe mutane tare da kayayyakinsu da ke sansanin.

Kamar yadda wata majiya ta tabbatar, an yi kokari wajen kashe wutar da gaggawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: