COVID-19: Gwamnatin Niger ta dage dokar kulle don a yi sallar Juma'a
- Gwamnan jihar Niger, Abubakar Sani Bello ya dage dokar kulle da hana zirga-zirga a jihar don a yi sallar Juma'a
- A makon da ya gabata ne gwamnan jihar Niger din ya saka dokar bayan samun mutum daya da aka yi a jihar dauke da cutar coronavirus
- Kamar yadda aka wallafa a shafin twitter din gwamnan, za a fara sallar Juma'ar ne daga karfe 11 na safe zuwa karfe 3 na yamma sannan dokar ta ci gaba da aiki
Gwamnan jihar Niger, Abubakar Sani Bello, ya dakatar da dokar kulle a jihar don a yi sallar Juma'a.
A makon da ya gabata, gwamnan ya saka dokar kulle ta makonni biyu don hana yaduwar cutar coronavirus a jihar.
Bello ya ce wannan matakin ya zama dole bayan an tabbatar da cewa wani mutum daya na dauke da cutar.
Amma kuma a ranar Juma'a, Lawal Tanko, jami'in yada labarai na sakataren gwamnatin jihar, ya ce za a yi sallar Juma'ar ne a karkashin matakai tsaurara.
DUBA WANNAN: COVID-19: Masari ya dakatar da sallar Tarawihi da Juma'a, ya kuma sake rufe wata karamar hukuma
Tanko ya ce za a yi sallar ne cikin mintuna 30 "za a ci gaba da kullen ana kammala sallar Juma'a".
"Ana amfani da wannan damar don sanar da al'ummar Musulmi a jihar Niger cewa an dage dokar kulle a jihar don yin sallar Juma'a a yau 17 ga watan Afirilun 2020," yace.
Ya kara da cewa, "Za a yi sallar Juma'ar ne a tsakanin karfe 11 na safe zuwa 3 na yamma a karkashin matakai tsaurara. Za a yi amfani da sinadaran kashe kwayoyin cuta, takunkumin fuska da kuma ruwa da sabulu don wanke hannu.
"Dokar nisantar juna za ta yi aiki sannan ba a amince da musabaha ba.
"Ana so a yi huduba da sallar a cikin mintuna 30. Ana shawartar Musulmi da su kiyaye wadannan dokokin don hana yaduwar annobar."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng