Covid-19: Dole mu sauya tsarin Tafsirin watan Azumi a bana - Malamai

Covid-19: Dole mu sauya tsarin Tafsirin watan Azumi a bana - Malamai

Mafi akasarin malaman addinin Islama a Najeriya, sun bayar da shaidar cewa ba zai yiwu su gudunar da tafsirin Al-Qur'ani da bisa al'ada su ka saba gudanarwa a watan Azumi ba.

Malaman sun ce yanayin da annobar cutar coronavirus ta jefa duniya a halin yanzu ya sanya suka dauki wannan mataki.

Gamayyar Malaman sun ce matakin da suka dauka ya yi daidai da kudirin gwamnatin kowace kasa a fadin duniya na hana tarukan jama'a domin dakile yaduwar cutar.

Haka kuma, malaman sun ce matakin jingine tafsirin biyayya ce ga dokar gwamnati.

A halin yanzu dai gwamnatin Najeriya ta dauki matakai daban-daban wajen kauce wa kamuwa da cutar corona, ciki har da kauracewa shiga taro da ta sanya a tilastawa 'yan kasar zaman gida.

BBC Hausa ta ruwaito cewa, daya daga cikin Shehunnan Malamai da suka dauki matakin dakatar da tafsirin a bana shi ne Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Covid-19: Dole mu sauya tsarin Tafsirin watan Azumi a bana - Malamai
Covid-19: Dole mu sauya tsarin Tafsirin watan Azumi a bana - Malamai
Asali: Twitter

Sheikh Bauchi yayin wani taron manema labarai da aka a gudanar a ranar Laraba ya ce, "ba za mu gudanar da tafsirin da muke yi a Kaduna ba inda daruruwan mutane suke halarta kowacce rana."

Shehin Malamin wanda ya kasance jagoran Darikar Tijjaniyya, ya ce zai rika gudanar da tafsirin a cikin gidansa da ke Bauchi, inda za a rika watsawa a kafofin labarai na sadarwa.

Ana iya tuna cewa, annobar corona ce ta sanya a watan Maris da ya gabata, Sheikh Bauchi ya sanar da jingine taron Maulidin Sheikh Inyas, wanda aka shirya gudanarwa a Sokoto da Abuja.

Shi ma dai babban Malamin nan na Sunna, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce ba zai gudanar da tafsirin azumin watan Ramalan bana ba a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna kamar yadda aka saba.

Sai dai Sheikh Gumi tamkar Shehun Bauchi, ya ce za a gudanar da tafsirin ne a wuri mafi dacewa a bisa tafarkin kiwon lafiya.

KARANTA KUMA: Ba duka 'yan Najeriya ne za a bai wa hasken lantarki kyauta ba - Gwamnati

Sheikh Gumi yana mai cewa ya dauki matakin hakan ne domin kare lafiyar kansa da kuma mutanen da ka iya halartar taron tafsirin, lamarin da ya ce yayi daidai da tsarin hukumomin lafiya na dakile yaduwar cutar.

Haka zalika babban malamin nan mai gudanar da tafsirin Al-Qur'ani cikin Kanon Dabo a kowace shekara, Sheikh Tijjani Bala Kalarawi, ya ce ba zai tara jama'a ba wajen tafsirinsa na bana ba.

Sheikh Kalarawi ya ce zai rika gudanar da tafsirin a cikin gidansa inda kuma za a watsawa al'umma ta gidajen talbijin, rediya da yanar gizo.

Sheikh Kalarawi ya yi kira ga sauran malaman da za su gudanar da tafsiri su yi koyi da irin su da suka yanke shawarar dakatar da tara jama'a kamar yadda gwamati ta bukaci a yi.

Shehin malamin na Kano ya kirayi sauran malamai da su yi koyi da irin wannan tsari na karantarwa a lokacin azumi domin kare al'umma daga harbin cutar corona.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng