Makonni hudu bayan kwantar dashi: Har yanzu dan Atiku Abubakar na dauke da cutar COVID-19

Makonni hudu bayan kwantar dashi: Har yanzu dan Atiku Abubakar na dauke da cutar COVID-19

Sakamakon gwaji na ci gaba da nuna cewa Mohammed Atiku Abubakar, dan tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, na dauke da cutar coronavirus.

Hakan na zuwa ne makonni hudu bayan an tabbatar da yana dauke da cutar ta COVID-19, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Har yanzu yana killace ba tare da ya nuna wata alama ta cutar ba, lamarin da ya sanya kwararrun likitoci cikin al’ajabi.

Mista Atiku-Abubakar, mai shekara 31, ya harbu da cutar a ranar 19 ga watan Maris. An dauke shi zuwa asibitin koyarwa na Abuja, inda ake kula da mafi akasarin masu COVID-19 a babbar birnin tarayya.

Makonni hudu bayan kwantar dashi: Har yanzu dan Atiku Abubakar na dauke da cutar COVID-19

Makonni hudu bayan kwantar dashi: Har yanzu dan Atiku Abubakar na dauke da cutar COVID-19
Source: Twitter

Duk da cewar yana kan shan magunguna da suka hada da, na inganta makaran kariyar garkuwar jikin sosai, amma duk da haka idan an gwada shi, sai jikin sa ya nuna har yanzu ya na da ita.

Ya shafe kwanaki 28 kenan ya na killace.

Wasu jami’an lafiya da suka yi martani bisa sharadin boye sunansu, sun ce ba su taba ganin mai irin wuyar sha’anin kamuwa ko warkewa da cutar ba, kamar Mohammed Atiku.

“Sakamakon gwaji ya sake nuna yana dauke da cutar a jiya,” in ji wani jami’in cibiyar. “Muna iya bakin kokarinmu domin tabbatar da ya samu lafiya, amma sai ya warke sannan za a iya sakin sa.”

“Mun ta fadin cewa wannan lamari na daban ne, amma muna da yakinin cewa zai warke kwanan nan,” in ji jami’in.

Chikwe Ihekweazu, shugaban NCDC, ya ki cewa komai game da halin da dan Atiku ke ciki a yammacin ranar Alhamis, 16 ga watan Afrilu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Allah ya yiwa tsohon Atoni-Janar na Kano, Aliyu Umar rasuwa

Mista Atiku-Abubakar ya tabbatar da cewar har yanzu yana a cibiyar killace wadanda suka kamu, amma ya ki cewa komai kan sakamakon gwajinsa da irin kulawar da yake samu.

A wani labarin, gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari ya sanar da dakatar da yin sallar tarawihi da sallar Juma'a a cikin jam'i.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel