An samu karin mutum 35 da suka kamu da coronavirus a Najeriya, jimmila 442

An samu karin mutum 35 da suka kamu da coronavirus a Najeriya, jimmila 442

Hukumar Kula da Cututtuka masu yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta tabbatar da samun karin mutum 35 da suka kamu da kwayar cutar COVID-19 wato coronavirus a kasar.

Hakan na nuna cewa jimillar wadanda suka kamu cutar a kasar ya kai 442.

A cewar hukumar ta NCDC sabbin wadanda suka kamu da cutar an samu 19 ne a jihar Legas, 9 a birnin tarayya Abuja, 5 a Kano sai biyu a jihar Oyo.

Hukumar ta bayyana hakan ne a shafin ta na Twitter mai lakabin @NCDCgov kamar yadda ta saba.

A karfe 10:20 na daren ranan Alhamis 16 ga watan Afrilu, an tabbatar da mutane 442 da suka kamu da #COVID19 a Najeriya.

Mutum 152 sun warke an sallame su yayin da mutum 13 sun mutu.

DUBA WANNAN: Shekau ya fadi maganin coronavirus a cikin sabon sakon sautin murya da ya fitar

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari ya sanar da dakatar da yin sallar tarawihi da sallar Juma'a a cikin jami kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Gwamnan ya kuma datse shige da fice a karamar hukumar Dutsinma na jihar inda aka samu bullar coronavirus a jihar a ranar Laraba.

Hakan na zuwa ne mako guda bayan Masari ya rufe garin Daura inda mutum na farko da aka samu da cutar a jihar ya rasu.

A cikin sakonni da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, ya bayar da umurnin rufe dukkan manyan kasuwanni a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel