Hanyar lafiya: Ainihin yadda ake amfani da tsummar rufe fuska ta kariya

Hanyar lafiya: Ainihin yadda ake amfani da tsummar rufe fuska ta kariya

Masana harkar lafiya sun bada shawarar cewa jama’a su rika amfani da tsummar rufe fuska domin kare kansu daga kamuwa da cutar Coronavirus da ke yawo a Duniya.

Hukumar NCDC mai alhakin takaita yaduwar cututtuka ta ce ya na da kyau a rika amfani da tsumar, amma mafi muhimmanci a rika wanke hannu da rage shiga jama’a.

The Cable a wani rahoto da ta fitar, ta yi karin haske game da yadda ake amfani da tsummar kariyar. Jaridar ta yi aiki ne da wasu shawarwarin da hukumar WHO ta bada.

Yaushe ake amfani da tsummar fuska?

Tsummar kariya ba dole ba ce, an fi bukatarta a lokacin da aka shiga cikin jama’a, misali a kasuwa inda mutum ba zai iya kauracewa kusantar mutane ba.

Ya ake fara amfani da tsummar fuska?

Kafin mutum ya soma amfani da wannan tsumma dole ya wanke hannuwansa da ruwa da sabulu ko kuma man goge hannu. Rashin hakan zai iya sa kwayar cuta ta shiga cikin tsummar.

KU KARANTA: Yadda cutar COVID-19 ta ke shiga sauran Jihohi daga Legas

Hanyar lafiya: Ainihin yadda ake amfani da tsummar rufe fuska ta kariya
Tsummar rufe fuska ta kan taimaka wajen hana kamuwa da COVID-19
Asali: UGC

Kuskuren wajen amfani da tsummar fuska?

Masana sun ce da mutum ya yi amfani da wannan tsumma a bai-bai, da ya ki amfani da ita duk marabarsu daya. Wurin da ya ke da launi ne ya kamata ya rufe hanci da bakin mutum. Ka da a bude hanci ko baki idan an sa tsummar, haka zalika dole a rufe dukkan kumatu.

Yadda ake cire tsummar fuska?

Idan za a cire tsummar daga fuska, ana cire ta ne daga baya ta yadda ba za a damalmala gaban ta ba. Ana kuma bukatar a guji taba hanci da idanu da baki a lokacin da ake cire tsummar. Dole a wanke hannuwa da zarar an rabu da wannan tsummar kariya.

Ana wanke tsummar fuska?

Da zarar an yi amfani da tsummar fuska sau daya, ana so a wanke ta tsaf da ruwan zafi.

Wadanda aka hana amfani da tsummar fuska?

Ba a so ayi amfani da wannan tsumma ga karamin yaron da bai wuce shekara biyu ba ko mai larurar numfashi ko kuma wanda ba zai iya cire tsummar a cikin sauki ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng