COVID-19: An bayyana yadda cutar ke fitowa daga Legas zuwa sauran jihohi

COVID-19: An bayyana yadda cutar ke fitowa daga Legas zuwa sauran jihohi

Shugaban fannin shiri na kwamitin shugaban kasa a kan yakar yaduwar annobar Coronavirus na kasa, Sani Aliyu, ya ce kwamitinsa ya matukar damuwa da rahoton yadda ake fitar da mutane daga Legas a sirrance.

A yayin tattaunawa a kan annobar Coronavirus a ranar Alhamis, Aliyu ya ce shige da fice tsakanin jihohi ne ke kawo yaduwar cutar.

Ya yi kira ga 'yan Najeriya da su karanta zirga-zirga don gujewa yaduwar cutar.

Jihohi da yawa dai a fadin kasar nan sun haramta shige da fice don gujewa yaduwar muguwar cutar.

"Zan yi magana a kan karanta yawo da kuma kara jaddada bukatar mutane su zauna a gidajensu ballantana a Abuja, Legas da Ogun.

"Ina so in janyo hankalin jama'a masu yawo tsakanin jihohi. An gano cewa cutar ta fi yaduwa a halin yanzu ta wurin masu yawo zuwa jihohi daban-daban," Aliyu yace.

"Akwai bukatar mu karanta tafiye-tafiye don hana yaduwar cutar coronavirus. Wannan jan kunnen ya biyo bayan gano cewa ana fitar da jama'a a manyan motocin daukar kaya daga Legas zuwa sauran jihohi," ya kara da cewa.

COVID-19: PTF ta bayyana yadda cutar fitowa daga Legas zuwa sauran jihohi
COVID-19: PTF ta bayyana yadda cutar fitowa daga Legas zuwa sauran jihohi
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Tsaro: Rundunar sojin Najeriya ta samu sabbin makaman zamani don yaki da Boko Haram

A bangaren Osagie Ehanire, ministan lafiya da kuma babban daraktan NCDC, Chikwe Ihekweazu, sun janyo hankulan jama'a da su dena gudun masu cutar.

Ihekweazu ya ce gudun masu cutar ne yasa suke tserewa tare da taimakawa yaduwar ta bayan sun gano suna dauke da ita.

"A lokacin da cuta mai karya garkuwar jiki ta shigo, hakan muka dinga yi. Amma wannan ba kanjamau bace, ba mummunan aiki ke kawo cutar ba.

"Ba alhaki bane yake kawo cutar. Masu dauke da cutar na da 'ya'ya, mata da iyalai. Suna bukatar karamci. Gudunsu na taka rawar gani wajen yaduwar cutar.

"Hakan na sa mutane su ki bayyana kansu koda kuwa sun san sun yi wata mu'amala da masu cutar. Daga nan su dinga yada ta," yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel