Dokar hana fita: Babu masakar tsinke a kasuwannin Kano

Dokar hana fita: Babu masakar tsinke a kasuwannin Kano

A yayin da bai wuce 'yan sa'o'i kalilan ba dokar hana fita ta fara aiki a fadin jihar Kano, al'ummar jihar sun yi kasuwanni tururuwa domin tanadin kayan bukata.

Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje, ya shimfida dokar hana fita a fadin jihar saboda yadda likafar annobar cutar coronavirus ta ke ci gaba da yaduwa a jihar.

Ganduje ya zartar da hukuncin hakan ne a daren Talata, 14 ga watan Afrilu domin takaita yaduwar cutar a jihar.

Yadda kasuwannin Kano suka tumbatsa yayin da dokar hana fita ke daf da fara aiki

Yadda kasuwannin Kano suka tumbatsa yayin da dokar hana fita ke daf da fara aiki
Source: Twitter

Dokar wadda za ta fara aiki a daren Alhamis ta mako daya ce kamar yadda Gwamnan ya bayyana.

A halin yanzu mutum 21 ne suka kamu da cutar a Kano bayan bullar ta karo na farko kwanaki biyar da suka gabata.

Hukumar lafiya ta jihar ta sanar da cewa, tuni mutum daya cikin wadanda cutar ta harba ya riga mu gidan gaskiya a daren Laraba.

Alkaluma sun tabbatar da cewa jihar Kano na daya daga cikin jihohin Najeriya wanda a baya-bayan nan aka samu bullar cutar.

Ya zuwa yanzu dai kamar yadda hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta bayyana, akwai jihohi 20 da cutar ta bulla, ciki har da babban birnin kasar.

KARANTA KUMA: Yadda mutum na farko ya shigar da cutar coronavirus jihar Kano - Likita

Haka kuma kungiyar malamai a jihar ta amince da dakatar da sallar Juma'a a duk ilahirin masallatan jihar yayin da dokar tilasta zamn gida za ta fara anjima kadan.

BBC Hausa ta ruwaito cewa malaman sun yi yanke hukuncin hakan ne bayan gudanar da taro a Africa House da ke fadar gwamnatin Kano a ranar Alhamis.

Legit.ng ta fahimci cewa, ungiyar malaman ta kasance wani rukuni a karkashin kwamitin kar ta kwana kan cutar covid-19 da gwamna na Kano ya assasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel