Shugaba Buhari ya taya Firayim Ministan Ingila murnar warkewa daga COVID-19

Shugaba Buhari ya taya Firayim Ministan Ingila murnar warkewa daga COVID-19

Kwanakin baya firayim ministan Birtaniya, Boris Johnson ya yi ta fama da Coronavirus har ta kai an kwantar da shi a dakin da ake ajiye wadanda ciwonsu ya yi kamari.

Daga baya an saki shugaban, ya kuma koma gida. A lokacin da Johnson ya ke jinya shugaban kasar Amurka Donald Trump da wasu takwarorinsa sun fito sun yi magana.

A halin yanzu shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya fito ya yi magana, kwanaki biyu da sallamar firayim ministan daga asibitin da ya yi ta faman jinya a Garin Landan.

Shugaba Muhammadu Buhari ya taya Johnson murnar samun sauki daga wannan muguwar cuta. An kwantar da Johnson mai shekaru 55 ne a wani asibiti na St. Thomas.

Shugaban Najeriyar ya aikawa kasar Birtaniya takarda ne a ranar Talatar nan 14 ga watan Afrilu, 2020. Muhammadu Buhari ya rubuta wasikarsa ne kai tsaye ga Boris Johnson.

KU KARANTA: Shahararrun Mutanen Afrika da annobar cutar Coronavirus ta kashe

Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya yi matukar farin ciki a sa’ilin da ya samu labarin an sallami Boris Johnson daga asibiti bayan an yi masa maganin cutar Coronavirus.

Mista Boris Johnson ya shafe kwanaki hudu ya na kwance a wannan asibiti da ke birnin Landan. A lokacin da shugaban ya ke jinya har sai da ta kai jikin na sa ya tabarbare sosai.

Buhari ya nuna farin cikinsa a wannan wasika da ya aika a farkon nan kamar yadda babban Hadiminsa Femi Adesina ya bayyana. Adesina ne mai magana da yawun shugaban.

Mista Femi Adesina ya kuma bayyana cewa shugaban kasar ya yi magana a madadin gwamnati da mutanen Najeriya domin yi wa firayim Ministan kasar Ingilan barkar samun lafiya.

Buhari a takardar ya kuma yi amfani da wannan dama wajen yabawa likitoci da sauran ma’aikatan wannan asibiti da su ka yi kokari wajen ganin shugaban ya samu lafiya.

“Na samu labarin murmurewarka cikin matukar farin ciki bayan an yi maka maganin cutar COVID-19.”

“Mu na taya ka godewa ma’aikatan asibiti da malaman lafiyan da su dage wajen ganin kai da wadanda ku kamu da cutar COVID-19 sun samu lafiya.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel