Lafiya uwar jiki: Dabarun karfafa garkuwan jiki don kare kai daga kamuwa da cutar Coronavirus

Lafiya uwar jiki: Dabarun karfafa garkuwan jiki don kare kai daga kamuwa da cutar Coronavirus

Sanin kowa ne annobar cutar nan ta Coronavirus ta karade yawancin kasashen duniya, kuma a duk inda ta shiga ta dauki rayukan mutane, kuma ta jikkata wasu da dama.

Alkalumma daga hukumar lafiya ta duniya WHO sun bayyana cutar Coronavirus ta kashe mutane 120,013 tun bayan bullar cutar a China a watan Disambar 2019 zuwa Afrilun 2020.

KU KARANTA: Coronavirus: Buhari ya zaftare kashi 9.1 daga farashin takin zamani don taimaka ma manoma

A nan gida Najeriya kuma mutane 407 ne suka kamu da cutar, yayin da ta kashe mutane 11, sai kuma mutane 95 da suka warware daga cutar.

Toh amma yayin da ake cigaba da tsumayin jiran binciko maganin cutar Coronavirus, ya dace a san hanyoyin yi ma kai kandagarki daga cutar, musamman karfafa garkuwan jikin dan Adam.

Garkuwan jikin dan Adam shi ne kadai yake iya maganin Coronavirus bayan ta shige shi, aikin ta kenan, shi yasa da zarar wata cuta ta shiga jiki, ita ke fara tasan masa don maganinsa.

Idan har garkuwan jiki ya zamana ba shi da karfi, tabbas ba Corona kadai ba, hatta sauran cututtuka da dama zasu yi tasiri a jikin dan Adam.

Lafiya uwar jiki: Dabarun karfafa garkuwan jiki don kare kai daga kamuwa da cutar Coronavirus

Lafiya uwar jiki: Dabarun karfafa garkuwan jiki don kare kai daga kamuwa da cutar Coronavirus
Source: Facebook

Wannan ne yasa muka kawo muku hanyoyin karfafa garkuwan jiki kamar yadda makarantar kiwon lafiya ta jami'ar Harvard ta wallafa:

- Kauce ma shan taba da sauran kayan hayaki

- Cin abinci mai kayan ganye

- Motsa jiki a kai a kai

- Rage kiban da ya wuce hankali

- Samun isashshen barci

- Tabbatar da tsaftar jiki da gabbai

- Rage damuwa a rai

Amma karfin garkuwar na raguwa da karuwar shekaru, don haka tsofaffi basu da garkuwa mai karfi, shi yasa ake bukatar su yawaita cin abinci masu sinadaran inganta garkuwan.

Kazalika akwai magungunan gargajiya da ake amfani dasu wajen inganta garkuwan jikin dan Adam domin yakar cututtuka a jikin, kamar su zuma, habbatissaudah da makamantansu.

Gwamnan jahar Oyo, Seyi Makinde ya tabbatar da haka, inda yace yayin da yake jinyar Coronavirus da ta kama shi, yana shan hadin Zuma da man habbatissaudah sau biyu a rana.

Sai ga shi daga karshe bayan kwanaki 6 kacal a killace ya fito da karfinsa, har ma ya koma bakin aiki a matsayinsa na gwamnan jahar Oyo.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel